Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce abun da kasar ke kashewa a bangaren bincike da kirkire-kirkire (R&D), ya karu da kaso 8.2 a mizanin shekara-shekara zuwa yuan triliyan 3.93, kimanin dala biliyan 584.5 a 2025.
A cewar Luo Qiushi jami’in hukumar NBS, cikin wa’adin shirin raya kasa na 14 daga 2021 zuwa 2025, matsakaicin abun da Sin ta kashe wa bangaren a shekara ya karu da kaso 10, kuma yanzu haka, kasar Sin ce kasa ta biyu a duniya mafi zuba jari a bangaren bincike da kirkire-kirkire. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














