Asbitin tafi da gidanka na jirgin ruwan sojin kasar Sin “Auspicious Ark,” wanda ke gudanar da shirin kiwon lafiya na “Mission Harmony-2026” ya isa Abidjan, babban birnin tattalin arziki na Cote d’Ivoire, a wata ziyarar sada zumunci da samar da hidimomin kiwon lafiya.
Wannan shi ne karo na farko da asibitin jirgin ruwan ya je kasar Cote d’Ivoire.Yayin ziyarar ta kwanaki 7, jirgin Auspicious Ark zai yi amfani da kayayyakin da yake da su wajen dubawa da jinyar marasa lafiya a yankin.
Haka kuma, karkashin shirin, an tura tawagar jami’an kiwon lafiya da tawagogin masu kafa asibitin tafi da gidanka zuwa asibitoci da jami’o’i domin musayar ilimi da bayar da hidimomin kiwon lafiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














