Yau Juma’a aka bude taron kasa da kasa na 2026 kan raya ilimin fasahohi da sana’o’in hannu a birnin Tianjin na Sin, inda wakilai daga kasashe da yankuna sama da 70 suka hadu domin tattauna makomar ilimin fasahohi da sana’o’i.
Taron bana mai taken “Ilimin sana’o’in hannu na duniya: rungumar sauyi tare, da tsara mizanin inganci tare, da kyautata makoma tare” ya kunshi zama na yankuna hudu a lokaci guda da ya hada kudu maso gabashi da kudancin Asia da na Asia ta tsakiya da Afrika da kuma Turai da Amurka, da zummar cimma daidaito kan raya ilimin sana’o’in hannu a fadin yankunan. Za a rufe babban taron gobe 17 ga wata. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)













