Jimilar Jarin Kai Tsaye Da Aka Zuba A Sin Daga Kasashen Waje Ta Kai Matsayi Na Biyu A Duniya
Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta ce bayanan da ta tattara daga rahoton shekara-shekara na 2025 kan jarin da aka zuba a kasar Sin daga kasashen waje tare da sassan da abin ya shafa, sun nuna cewa, jimilar kudaden jari na kai tsaye da aka zuba daga kasashen waje, ya kai yuan tiriliyan 26.8. Hakan ya nuna ci gaba cikin shekaru shida a jere, kuma ya kai matsayi na biyu a duniya. Ma’aikatar ta sanar da hakan ne yau Alhamis, yayin taron manema labarai na yau da kullum. Ban da haka kuma, ma’aikatar kasuwancin ta sanar da cewa, kashi na farko na bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasa da kasa na kasar Sin, wato “Canton Fair” karo na 140, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Guangzhou na kasar Sin, ya mayar da hankali kan kayayyakin masana’antu na zamani. A wannan matakin, kamfanoni 12,000 suna nuna fasahohin zamani game da fasahar AI da kare muhalli da sauransu. Ma’aikatar ta kara da cewa, Sin za ta ci gaba da aiki tare da bangaren Turai don amfani da tsarin tattaunawa kan fitar da kayayyaki, ta yadda za a bunkasa cinikayyar kayayyaki tsakanin bangarorin biyu. Bugu da kari, ta ce fahimtar da aka cimma tsakanin Sin da Turai game da ababen hawa masu amfani da makamashin man fetur da lantarki, zai samar da moriya ga bangarorin biyu.(Safiyah Ma)



















