A yau Alhamis, firaministan Sin Li Qiang, ya gana da shugaban Botswana Duma Gideon Boko da shugaban majalisar ministocin Togo Faure Essozimna Gnassingbe, daya bayan daya a birnin Beijing.
Haka kuma a yau din, Sin da Togo sun fitar da sanarwar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin janhuriyar jama’ar Sin da gwamnatin janhuriyar Togo, kan gina al’ummar Sin da Togo mai makoma ta bai daya a sabon zamani. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














