An yi bikin kaddamar da cibiyar bincike ta Sin da Afrika a Afrika ta Kudu, tare da wani taron kara wa juna sani kan “Hada Hannu Tsakanin Kasashe Masu Tasowa Domin Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya ga Dan Adam,” jiya Talata a kwalejin horar da ma’aikatan gwamnati ta Afrika ta Kudu (NSG) da ke birnin Pretoria, fadar mulkin kasar.
Mataimakin shugaban kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin Peng Jinhui da mai rikon mukamin shugaban kwalejin NSG Phindile Mkwanazi da jakadan Sin a Afrika ta Kudu Wu Peng ne suka yaye labulen cibiyar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














