Xi Ya Yi Kira Da A Wanzar Da Kokarin Fadada Da Karfafa Ci Gaban Fannin Kere-kere
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a wanzar da kwazo domin fadada, da karfafa ci gaban fannin kere-kere, ta yadda za a samar da goyon baya mai karfi ga bunkasa zamanantarwa irin ta kasar Sin. Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya bayar a baya-bayan nan, wanda aka gabatar a yayin taron kasa kan batun bunkasa kere-kere, wanda ya gudana jiya Laraba da yau Alhamis a birnin Beijing. Shugaba Xi, ya ce ya kamata a kara azamar tabbatar da ci gaba mai inganci, da tsaro bisa matakin koli, da samar da ci gaba mai kunshe da basira kana marar gurbata yanayi, a kuma mayar da tsarin hada-hadar masana’antun kasar Sin mai karin dogaro da kai da juriyar hadurra. Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada bukatar gaggauta bunkasa zamanantar da tsarin ayyukan masana’antu ta hanyar ingiza kere-kere a matsayin kashin bayan hakan, da karfafa tushen sashen tattalin arziki mai nasaba da sarrafawa, da hada-hadar sayar da hajoji da hidimomi. (Saminu Alhassan)



















