Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing
A jiya Talata ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya gabatar da jawabi, a liyafar da aka shirya don nuna maraba da baki mahalarta taron dandalin tattaunawa na Xiangshan da ake gudanarwa kan sha’anin tsaro a birnin Beijing karo na 13, inda wakilai daga kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin duniya kusan 100 suka halarta. A jawabin da ya gabtar, ya ce duk da kalubalen da duniya ke fuskanta a halin yanzu, manufar samar da zaman lafiya, bunkasa ci gaba, hadin gwiwar kasashe, da samun nasara ga kowane bangare, abu ne da ba za a iya dakatar da shi ba, sannan babu ja da baya kan yanayin da ake ciki na samun bunkasar kasashe daban daban da dunkulewar tattalin arzikin duniya wuri guda. Han Zheng ya jaddada bukatar kiyaye manufofi da dokokin MDD, da tsayawa kan ingantaccen tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, sanya bukatar al’umma a gaba da kome, da kuma tabbatar da cewa fasahohi sun zama abin moriya ga cigaban dan Adam. Ya kara da cewa a a matsayin Sin na babbar kasa kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a kullum tana sanya ci gabanta ne domin bunkasa rayuwar dan Adam, da kuma ba da gudunmawarta domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kuma ci gaba ta hanyar zamanantar da kanta. Har ila yau, yayin da ake bikin bude taron dandalin Xiangshan na Beijing karo na 13 a yau Laraba, minitan tsaron kasar Sin, Dong Jun ya jaddada batun kiyaye kwanciyar hankali a bisa tsarin mabambantan bangarori. Dong ya yi kira da a ci gaba da yin riko da tsarin mabambantan bangarori na hakika, da kafe kai da fata wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin MDD, da kuma tsarin duniya da aka shimfida bisa dokokin kasa da kasa. Kazalika, Dong ya jaddada bukatar sanya darussan da aka koya daga tarihi a cikin zukata da ci gaba da sa-ido sosai game da babakeren wata kasa, da tara karfin soji da kuma maimaita tarihi. Dong ya yi nuni da cewa, darussa masu daci da aka koya daga yake-yaken duniya da bala’o’in rikice-rikice da hargitsin da ake fama da su a yau, suna gargadi ne kan cewa rigakafin barkewar rikici dabara ce mafi muhimmanci a bangaren tafiyar da sha’anin tsaro.



















