Kasar Sin ta amince tare da fitar da jerin ka’idoji irinsa na 3, na na’urar kiwon lafiya mai sadarwa tsakanin kwakwalwa da na’ura da ake kira da
Jerin ka’idojin shi irinsa na farko a duniya na na’urorin BCI na kiwon lafiya masu amfani da fasahar AI wajen sarrafa sakonnin da kwakwalwa ke fitarwa.
Fasahar BCI tana samar da damar sadarwa kai tsaye tsakanin kwakwalwar dan adam da ta dabbobi da na’urori.
Kuma ta hanyar samu da fahimtar sakonni daga kwakwalwa, na’urar BCI za ta bayar da damar sadarwa tsakanin kwakwalwa da na’ura, lamarin da zai ba na’ura mai ruwa da tsaki damar aiwatar da abubuwan da aka yi niyya a cikin kwakwalwa.Hukumar kula da kayayyakin kiwon lafiya ta kasar Sin ce ta fitar da ka’idojin, wadanda suka zayyana bukatun inganci da dabarun tantance bayanan sakonnin kwakwalwa da tsarin lissafi na AI ke amfani da su a na’urorin BCI. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














