Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS
Daga ranar Litinin 26 zuwa Alhamis 29 ga watan nan, kwamitin tsakiya na 20 na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, zai gudanar da cikakken zama na biyar a birnin Beijing. Zaman na wannan karo zai karkata ga tattauna manyan batutuwa dake shafar wanzar da cikakken ci gaba, da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai na jamiyyar kwaminis. A matsayinta na jamiyya mai mulkin kasa, JKS na gudanar da taron kasa a duk shekaru biyar domin zaben sabbin membobin kwamitin koli, wadanda ke daukar nauyin jagorancin aikin dukkanin jamiyyar tsakanin tarukanta. Kazalika, taron na yin nazari da gabatar da manyan batutuwan jamiyya da kasa ta hanyar kiran cikakken zama na kwamitin tsakiya. Bisa tanadin kundin mulkin jamiyyar, kwamitin tsakiya yana gudanar da cikakken zama a kalla sau daya a duk shekara. Cikakken zama na biyar na kwamitin tsakiya na 20 na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne cikakken zama karo na biyar da membobin kwamitin kolin JKS da aka zaba a yayin cikakken zaman jamiyyar na shekarar 2022 suka kira. A shekarar nan ta 2026 ne ake bikin cika shekaru 105 da kafuwar JKS, kana a banan aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, a gabar da ake dada ingiza cikakkun ayyukan sauye-sauye da samar da ci gaba a dukkanin sassa. Kiran cikakken zama na biyar a wannan muhimmin lokaci, mai jigon "cikakken ci gaba da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai na jamiyyar kwaminis" a matsayin babbar ajandarsa, na nuni ga yadda jamiyyar kwaminis ta kasar Sin ke wanzar da muhimmin tsari na dogon lokaci da nufin karfafa gina kai. Bayan tafiya mai tsayi ta shekaru dari, JKS ta wanzar da ingiza ci gaba, da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai, tana iza kanta, da samarwa kai karfi na hakika, mai ruhin yiwa kai kwaskwarima. Wannan ba wai tabbaci ne kadai na asali a fannin nasarar siyasa ga JKS wajen sarrafa akalar aikin zamanantarwa mai halayyar musamman na Sin, da kare babban kudurin sake farfado da kasa ba ne, har ma wani muhimman sirri ne ga duniya, ta yadda za ta iya fahimtar fifikon tsarin jagorancin kasar Sin, da cikakken salon ci gaban kasar na dogon lokaci da daidaito dake gudana bisa tsari. (Saminu Alhassan)



















