Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun kara amincewa da kasancewar iko tsakanin kasashe daban daban a duniya. Kuma bangaren Sin ya yi imanin cewa, ba za a iya dakile wannan ci gaban da duniya ta samu ba.
Da ya tabo batun sanya na’urar Buoy da Sin ta yi cikin ruwa don duba yanayin cikin tekun da batun ya shafa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan ya dace da dokokin cikin gida na kasar Sin da kuma dokokin kasa da kasa.
Guo Jiakun ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai kwazo da himma wajen tunkarar sauyin yanayi, kuma za ta cika alkawarinta na cimma burin “daidaita abubuwa masu dumama yanayi da rage fitar da su” bisa hanyoyin da ta zaba. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp