ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Baje Kolin Motoci Na Kasa Da Kasa A Beijing Ya Haska Makomar Masana’antar Motoci

by Sulaiman and CGTN Hausa
5 months ago
Motoci

Bikin baje kolin motoci na kasa da kasa na Beijing na shekarar 2026 ya kasance wani muhimmin lamari da ya bayyana yadda masana’antar kera motoci ta duniya ke canzawa cikin sauri.

Wannan baje koli ba kawai ya kasance wurin baje sabbin motoci da ake kerawa da fasahohin zamanin yanzu da kuma rayuwa ta gaba ba ne, har ma ya haskaka mana girman ci gaba, da kyakkyawan buri, da kuma tasirin da wannan masana’anta ke da shi a yau da kuma hangen gobe.

Abu mafi daukar hankali shi ne yadda bikin ya jawo dimbin kamfanoni na cikin gida da na ketare, lamarin da ke kara tabbatar da Beijing a matsayin cibiyar kirkire-kirkire a duniya.

ADVERTISEMENT

Manyan kamfanoni masu tarihi da sabbin da ke tasowa cikin hanzari, sun baje nau’o’in motoci da ke nuna gasa mai tsafta da kuma yanayi mai cike da kuzari a bangaren kere-keren motoci da amfani da fasaha kana da gogayyar samarwa.

Motocin lantarki su ne suka mamaye sahun gaba, inda aka gabatar da sabbin samfura masu ingantaccen baturi da kuma fasahar tuki mai cin gashin kansa.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

Kazalika, motoci masu tashi kusa da doron kasa wanda dimbin jama’a suka fi karkata hankulansu a kewayen rumfunansu, sun nuna yadda sufurin motoci zai kasance a gaba.A bangaren motocin alatu, an baje sabbin motoci masu tsare-tsare na jin dadin rayuwa har da na tafe-da-gidanka da ke dauke da kayan amfanin gida kamar su wurin bacci, sashen girki har da mazaunin kiwon dabbobi na gida.

Haka nan, akwai motoci na kadaran-kadahan, watau masu saukin kudi wadanda su ma aka tsara su ta yadda za su dace da bukatun jama’a da dama.

A gefe guda kuma, yawan tururuwar jama’a a bikin baje kolin ya kayatar matuka wanda a da, na zaci tun da ana cikin hutun ranar ’yan kwadago, watakila za a samu karancin masu halarta saboda tafiye-tafiye.

Bugu da kari, salo daban-daban na tallace-tallace da kamfanoni masu baje kolin motocinsu suka yi amfani da su a rumfunansu ciki har da kide-kide da wasanni masu jawo hankula har ma da raba kyaututtuka, sun nishandatar da mahalarta sosai.

Bisa bayanin da na kalato, an kafa bikin baje kolin motoci na kasa da kasa na Sin ne wanda aka fi sani da “Auto China” a shekarar 1990, kuma tun daga wancan lokaci ya zama daya daga cikin manyan baje kolin motoci da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu.

A matsayinta na daya daga cikin kasuwanni mafi girma na motoci a duniya, kasar Sin tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kere-keren motoci masu fasahohin zamani da ke amfani da sabbin makamashi masu kiyaye muhalli.

An gudanar da baje kolin ne a sabon dandalin baje koli na Capital International Exhibition Center da kuma na China International Exhibition Center Shunyi Hall, inda aka mamaye filayensu masu fadin murabba’in mita fiye da 380,000 da tsare-tsare na baje koli masu ban sha’awa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Motoci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu
  • Sulaiman
    Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana
  • Sulaiman
    Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali
Motoci
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Kammala Taro Na 13 Na Dandalin Tattauna Tsaro Na Xiangshan A Beijing
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mataimakin Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Na 23
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Fitar Da Shirin Shekaru 5 Ya Bude Sabo Babi Na Tsarin Ci Gaban Yankin HK

MASU ALAKA

Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu
Daga Birnin Sin

Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

September 18, 2026
Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

September 18, 2026
Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

September 18, 2026
Next Post
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Gudanar Da Sahihin Zaɓe — Shugaban INEC

Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026
Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

September 18, 2026
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

September 18, 2026
‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

September 18, 2026
Samun Ci Gaba Shi Ne Abu Mai Tushe Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam

Samun Ci Gaba Shi Ne Abu Mai Tushe Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam

September 18, 2026
Gwamnatin Najeriya Na Daukar Darasi Daga Salon Da Kasar Sin Ke Amfani Da Shi Na Kulla Alakar Diflomasiyya Ta Hanyar Jan Hankali Da Kyakkyawar Mu’amala

Gwamnatin Najeriya Na Daukar Darasi Daga Salon Da Kasar Sin Ke Amfani Da Shi Na Kulla Alakar Diflomasiyya Ta Hanyar Jan Hankali Da Kyakkyawar Mu’amala

September 18, 2026
ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

September 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.