Dan wasan tsakiyar Manchester City da Spain Rodri ya sauya akalarsa zuwa Fc Barcelona yayinda yaki amincewa da tayin komawa Real Madrid da akayi mashi, yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na duba yiwuwar daukar tsohon dan wasan na Athletico Madrid idan aka cimma matsaya tsakanin kungiyoyin biyu.
Rodri Mai shekaru 30 ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar kofin Duniya da aka kammala a kasashen Amurka, Mexico da Canada wanda kasarshi ta Spain ta lashe bayan doke Argentina daci 1-0, a cewar dan jarida Gerard Romero, Rodri ya amince da komawa kungiyar ta Catalonia, wanda hakan ya share fagen tattaunawar da Barcelona ta fara yi da Manchester City din.
An yi ta danganta Rodri da komawa Real Madrid, inda aka ruwaito cewa kungiyar kwallon kafar ta kasar Spain ta cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiyar tare da tattaunawa da Manchester City kan yiwuwar yarjejeniyar, amma jinkirin cimma yarjejeniyar ya bude kofa ga Barcelona, wadda kuma yanzu da alama ta sami tabbaci daga Rodri wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya (Ballon D’or) a shekarar 2024.














