A kwanakin baya ne, kafafen yada labarai na cikin gida da na kasashen waje suka kasance cike da labaran gurfanar da kananan yara da babbar kotun tarayya ta yanke masu hukuncin cin manar kasa saboda gudanar da zanga-zangar kawo karshen rashin gudanar da shugabanci na gari a Nijeriya da kuma sauran aikata laifuka.
Wani babban abin takaici shi ne, yadda kafafen yada labarai na kasashen waje suka wallafa cewar, gwamnatin kasar nan, za ta yankewa su yaran 29 hukuncin kisa saboda gudanar da halin yunwar da aka shiga a kasa.
- Gwamnatin Kano Ta Miƙa Yara 76 Da Aka Kama Yayin Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Biyan Bashin Waɗanda Aka Tsare A Gidan Gyaran Hali
Sai dai kuma, wasu kwararrun Lauyioyi da kungiyoyin kare rajin ‘yancin ‘yan Adam a kasar, sun fito karara sun yi tir da kama yaran da mahukuntar kasar suka yi kan gudanar da zanga-zangar, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda wasu daga cikin yaran da aka gurfanar a gaban babbar kotun tarayya bayan an gurfanar da su a gaban kotun domin bukatar bayar da belinsu.
Kazalika ma, lamarin ya kuma kara yamutsewa hakan ya biyo bayan zargin da aka yi na cewa, a lokacin da suke tsare a hannun ‘yan sanda, sun ci zarafin su, wadanda kuma ‘yan sandan suka mayar da su tamkar wadanda suka aikata wani babban laifi.
Makomar wadannan yaran dai, tasa tunawa da zanga-zangar #EndSARS wadda wasu jami’an tsaro suka yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin masu zanga-zangar a lokacin da suke kan yin zanga-zangar.
Me yiyuwa sukar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sha ne, ya tilasata shi bayar da umarni nan take, da a saki yaran a kuma gaggauta mika su ga iyayensu.
A nan, muna jinjinawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ceto rayuwar yaran daga hannun jami’an tsaron, musamman ma idan aka yi la’akari da irin wahalar da suka sha a hannun ‘yansanda.
A bisa tunanin, tun da farko bai kamata ma ace ‘yan sandan sun kama yaran ba, domin yaran dai, sun yi zanga-zangar ce kan kuncin rayuwa.
Zaman da yaran suka yi a kulle, hakan ya nuna cewa, an barsu ne a cikin yunwa da kasancewa a cikin rashin lafiya don kawai sun gudanar da zanga-zangar fargar da gwamnati kan ci gaba da kasancewar talakawan kasar, a cikin kangin talauci.
Kwanci tashi, irin juyin juya hali da ya auku a kasar Faransa, ya janyo kifar da masarautar garjiya ta kasar, musamman ma, ba wai don samun yawan talauci ba, amma saboda irin mulkin gurguzu da masarautar ke yiwa ‘yan kasar.
Kazalika ma, kasar Rasha ba wai an kifar da gwamnatin kasar ne da makamin kari dangi ne ba, abin ya kawo karshen shugabannin kasar ba, amma boren da ‘yan kasar suka gudanar ne, ya kawo karshen shugabancin mahukuntar kasar, ya biyo bayan jefa rayuwarsu a cikin kangin rikcewar rayuwa.
Namu ra’ayin a nan shi ne, akasarin kasashe ba su koyon darasi a kan kuskuren da wasu kasashen suke tabkawa.
Abinda ke faruwa a Nijeriya shi ne, kusan matakan da bangaren gwamnatoci uku na kasar ke yi, ba su daukar kwararan matakan da suka dace.
Duk kasar da ta kasance kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum sun fi karfin talakan kasar, amma masu rike da madabun iko na siyasa, suna yin wandaka da watanda da kudaden gwamnati yadda suke so, suna kuma barin ‘ya’yan talakawa a cikin kangin halin yunwa, wannan babban abin bakin ciki ne.
Ra’ayinmu a nan irin yadda yaran suka tsinci kansu a cikin cin zarafin gwamnatin su, wadda ya kamata ta nuna cewa, mulkin dimokiradiyya ne ake gudanarwa a kasar hakan kuma ya nuna cewa, tamkar ana gudanar da mulkin mallakar Fir’aunanci ne a kasar.
A matsayin a wannan jaridar, mun nuna taikaicin mu a kan irin halin da yaran suka tsinci kansu a lokacin da aka tsare su, wanda kuma jami’an tsaro suka dauke su tamkar wasu masu mugun hadari a cikin alumma.
A bisa tunanin mu, irin wannan halin da aka jefa yaran a ciki, hakan zai iya juya tunanin su zuwa rungumar munanan dabi’u.
Ya zama wajbi mu ankarar da mahukunta don su gane cewa, ya kamata su san yadda za su rinka tafiyar da yara a duk lokacin gudanar da wata zanga-zanga, kamar dai irin ta #EndBadGobernance.