Kwanan nan, Firaministar kasar Japan Sanae Takaichi, ta aike da hadaya zuwa haikalin Yasukuni, sannan ministan manufofin tattalin arziki da kasafin kudi na kasar ya ziyarci wurin, lamarin da ya jawo Allah wadai daga al’ummar duniya baki daya.
Wani binciken da kafar CGTN ta gudanar ta kafar yanar gizo ya nuna cewa kashi 90.71 cikin 100 na masu amsa tambayoyin binciken a fadin duniya sun yi kira ga kafofin watsa labarai na duniya da su yi amfani da kalmar “haikalin masu laifukan yaki”, yayin da suke yada labarai kan batun haikalin Yasukuni, domin su tunatar da jama’a bukatar yin taka-tsan-tsan da farfadowar ra’ayin nuna karfin soja na kasar ta Japan.














