Sha’anin tafiyar da jagorancin duniya ya sake shiga wani “zamani na kungiyar SCO”. A yayin gudanar da taron kolin Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekarar 2026, wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar tare da hadin gwiwar Jami’ar Renmin ta kasar Sin, ta hannun Cibiyar Nazarin Sadarwa ta Duniya a Sabon Zamani, ya nuna cewa, daga cikin mutane 13,707 da suka bayyana ra’ayoyinsu a kasashe 48 na duniya, kashi 74.6% sun yi amannar cewa SCO tana samar da kyakkyawar hanya domin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tsarin gwamnatoci daban-daban tare da zama wani muhimmin karfi na zurfafa sabon nau’in dangantakar kasa da kasa da kuma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dukkan bil’adama.
A matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar SCO, kasar Sin ta ci gaba da alakanta ci gaban kanta da na kungiyar SCO. Kashi 76.2 na wadanda suka bayyana ra’ayoyin sun bayyana cewa, shirin kasar Sin na shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)” ya samar da sabon yanayi na ci gaban duniya mai alaka da kuma hadewa da juna; yayin da kashi 73.5 na mutanen kuma suka yi nuni da cewa, shawarar “inganta jagorancin duniya (GGI)” yana nuna hanya ga kasashe masu tasowa don su shiga a dama da su wajen yin garambawul ga tsarin tafiyar da jagorancin duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














