Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir ya kaddamar da rabon tallafin Naira 50,000 ga mata 5,200 kowacce daya da aka zabo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin a gidan gwamnati da ke Kano a ranar Talata, gwamnan ya ce kudaden da suka kai Naira miliyan 260, za a raba su ne a duk wata ga sabbin dauka 5,200 har zuwa karshen wa’adin mulkinsa.
- Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Yawan Jima’i A Benuwe
- Boko Haram Na Amfani Da Na’urar Starlink Ta Elon Musk Wajen Sadarwa Ta Yanar Gizo
A cewarsa, an kirkiro shirin tallafin ne don taimakawa iyaye mata wajen fara kasuwanci domin rage nauyin iyali.
Yusuf ya bayyana cewa, shirin wanda kwamitin sake wayar da kan al’umma, CRC ya shirya, ya kunshi tallafawa mata 100 a duk kananan hukumomi 36 da ke yankunan karkara da kuma mata 200 a duk kananan hukumomi 8 na jihar.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, tallafin an yi shi ne don biyan tukuici ga mata bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar don samun nasararsa a zaben 2023.