A ranar 31 na watan Oktobar 2025, Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimeen JNIM, ta yi ikirarin cewa, ta kaddamar da kanta cikin kasar nan.
Wannan ikirarin na ta, ya nuna tsagwaron sakacin da aka yi a fannin tsaron kasar, musamman duba da yadda kungiyar, masu tsatsauran ra’ayi, har suka iya kutse a cikin kasar.
- Akwai Bukatar Karfafa Hadaka Domin Ciyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa Gaba A Afirka —Dantsoho
- Sin: Kome Zai Samu Yankin Taiwan Babu Ruwan Kasar Japan
Kungiyar wadda ke da akida irin ta Kungiyar Ta’addanci ta Al-Kaeda, ta shelanta cewa, ta hallaka Sojin kasar daya, yayin da ‘ya’yanta, suka yi wa tawagar dakarun soji, kwanton Bauna a Iyakar kasar Benin.
Kazalika, wannan kutsen na kungiyar, ya nuna karara na irin sakacin tsaron kasar nan da har ayyukan kungiyar, ya tsallake yankin Sahel zuwa Afrika ta Yamma.
Za a iya cewa, ta yi wannan kusten daidai da lokacin da Nijeriya, ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro da kuma yadda wasu kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi ke kai hare-hare kan wasu ‘yan kasar.
A nan, wannan Jaridar na yin mamaki kan yadda kungiyar ta As JNIM mai alaka da Al-Kaeda ke kara ba za ayyukanta a cikin kasar.
A saboda hakan Jaridar na ganin ya zama wajbi mahukuntan tsaron kasar, da su tabbatar da sun karfafa tsaro, a iyakokin kasar
Kungiyar ta JNIM, an kirkiro da ita ne, a watan Maris na 2017, wadda kuma ta yi hadaka da kungiyar Al-Kaeda.
Bugu da kari, Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ayyana kungiyar ta JNIM, a matsayin wani reshe na Al-Kaida, da ke a kasar Mali.
Zallaka, Gidauniyar kafar yada labarai ta JNIM, ta yi wallafa ikirarin cewa, dakarun kungiyar sun samu nasarar yiwa sojojin kwanton Bauna ta hanyar dasa Bam a Iyakar Benin, wanda hakan, ya janyo mutwar soja daya.
Wannan ayyukan ta’addancin kungiyar, ya yi daidai da, irin salon da ta yi watan Yulin 2025, wanda ta kai hare-haren da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 54 a kasar Burkina Faso, wasu 36 a kasar Mali, da kuma wasu bakwai, a Jamhuriyyar Nijar, ta hanyar yin amfani da Iyakar Markoye.
Kazalika, kungiyar na yin amfani da Jirage marasa matuka, wajen kai hare-harensu, wadda kuma Al-Kaeda ce, ke tallafa wa mata da makamai da kuma kudade, domin aikata ta’asarsu.
Iyakar Benin da Nijeriya, ta kasance, wata mashiga ta yin fasakwarin makamai da muggana kayan maye, wanda hakan ya zama babbar hanyar da kungiyar ke yin amfani da ita.
Wani rahoton ta UNODC ta fitar a 2025 ya nuna cewa, an kiyasta cewa, an shigo da kaso 70 na kananan makamai ta Iyakar Benin da Nijeriya,
Hakazalika, wani rahoton Bankin Duniya ya sanar da cewa, talauci, ya Arewacin Nijeriya, ya sanya irin wadannan kungiyoyin ta’addacin daukar hayar wasu shiga cikin irin wadannan kungiyoyin ta’addancin.
Wannan Jaridar na da yakin cewa, domin a dakile ayyuan kutsen irin wadannan kungiyoyin ta’addancin, ya zama wajbi mahukunta a kasar nan, su amfani da kimiyyar fasahar zamani wajen tabbatarwa da karfafa tsaro, a iyakon kasar.
Bugu da kari, ya zama wajbi, a sanya na’urorin zamani na sanya ido da kuma yin amfani da Jiragen sama, marasa matuka domin tabbatar da tsaro.
Kazalika, ya kamata mahukuntan kasar, su yi koyi da salon da jihar Sokoto ta kirkiro da shi, na karrarfafa tsaro a iyakokin jihar.
Ya kuma kamata a yi amfani da salon kungiyar ECOWAS, na gudanar da aikin sintiri na hadaka domin dakile shigorar ‘yan ta’adda daga yankin Sahel inda kwararowarsu, ta kai kaso da shigo da makamai, ta kai 60.
Bugu da kari, akwai bukatar a zuba kudade masu dimbin yawa a shekarar 2026, cikin Cibiyar Dakile Shigo da Kananan Makai ta kasa, tare da kuma tabbatar da ana yin aiki kafada da kafada a tsakanin Hukumomin Tsaro, musaman domin a dakile kutsen kungiyoyin ‘yan ta’adda zuwa cikin kasar nan.
Haka, ya kamata mahukunta a kasar, su kirkiro da shirye-shiye a cikin alumma, kamar dai a jihar Borno, domin a bai wa matasa horon koyon sana’aion hannu domin kare su, daga jan ra’ayin kungiyar ‘yan ta’adda na shiga cikin kungiyoyin.
Da irin wannan salon jan ra’ayin wasu matasan ne, har ta kai ga kungiyar Al-Kaeda ta yi fice, wajen janyo matasa a cikinta.
Wasu daga cikin kwararru, musamman da ke yin fashin baki kan aukuwar rikice-rikice, suna ganin yin yafiya ga ‘yan ta’adda da suka tuba suka kuma ajiya makamansu, hakan zai taimaka, wajen rage aikata ta’addanci.
Duba da yadda kungiyar ta JNIM da ke da alaka da Al-Kaeda, ta yi kutse a cikin kasar nan, ya zama wajbi, mahukunta a kasar, su dauki matakan gaggawa domin a taka mata birki, wanda hakan zai bai wa kasar samun cikakken ikon bai wa iyakon kariya.














