Ci gaba da samun karuwar hare-hare kan al’umomin da ke a garurunwan iyaka da jihar da wasu jihohi, lamarin na kara jefa fargaba a cikin jama’a.
A saboda haka, akwai matukar bukatar a hada karfi da karfe, domin a kawo karshen kalubalen rashin tsaro, da tuni, ya zamowa kasar tamkar wani karfen Kafa, musamman a jihohin da ke a Arewa ta Yamma da kuma a jihohin da ke a Arewa ta Tsakiya
- Tinubu Da Shugabannin ECOWAS Sun Gudanar Da Taron Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau
- Sarkin Musulmi Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Kazalika, wasu alumomin da ke a jihohi kamarsu, Zamfara, Katsina, Kebbi da Sokoto, na ci gaba da kokakwa, kan yawan hare-haren da ‘yanbindiga ke kai masu, ind hare-haren, suka auka a wasu yankuna na Shanono da ke a Kano, wanda suke da iyaka da, musamman Katsina.
Sai dai, wasu da ke a cikin alummomin na garin Shanono, sun tabbatar da cewa, tun a 2022 ne, ake kai masu hare-haren, inda a yayin hare-haren, aka kashe wasu, wasu kuma aka tarwatsasu daga matsugunansu, wasu kuma aka sace Sahnunsu.
Hakazalika, abin bakin ciki ne, kan samu karuwar hare-haren a Tsanyawa, Shanono, Bagwai, Gwarzo, da Karaye, da ke a iyaka da Katsina, inda lamarin, ya kuma ba zu, daga Katsina zuwa Kano.
Bugu da kari, an ci gaba da samun karuwar kai hare-hare da kuma yin garkuwa da mutane a yankin Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono, wanda har da wasu mata da aka sace.
Aukuwar hare-haren, sun sanya alumomin da ke a yankunn Tudun Fulani, Malami, Unguwar Kudu, ’Yan Kwada, Santar Abuja, Kulki, Unguwar Tsamiya da Goron Dutse, da sauransu, tserewa, daga matsugunansu.
Wani abin takaicin shi ne, duk da yin yarjejeniya samar da zaman lafiya da wasu alumomin da ke a jihar Katsina, inda akalla kananan hukumomi 18, suka kulla wannan yarjejiniar da ‘yan bindigar, amma sai hare-haren, suka kara zafafa.
Ayar tambaya a nan ita ce, idan har da gaske ne, wannan yarjejeniyar, da gaske ne, amma mai ya sanya, ‘yan bindigar suka karkatar da Akalarsu, zuwa kai hare-hare a jihar Kano?
Hakan ya nuna a zahairi cewa, kulla yarjejeniyar da ‘yan bindigar tamkar alumomin, sun hakawa kawunansu, wani Kabari ne.
Karin wani abin dubi shi ne, yadda daukacin ‘yanbindigar, suka halarci wajen kulla yarjejeniyar, sabe da muggan makamansu, a kafada.
Mun sha fada ba tare da wata tamtama ba cewa, mafita kan wannan matsalar ta rashin tsaron shi ne, hukumomin tsaron kasar, su kara kaimi wajen kai hare-hare kan ‘yan bindigar, domin kawo karshen ayyukansu na rashin imani.
Idan har mahukunta suka ci gaba da yin sakaci kan ci gaba da samun karuwar ayyukan ‘yanbindigar a Kano, ba fata ba, idan ba a yi a hankali ba, lamarin zai iya munana, fiye da na jihohin Zamfara, Kebbi da Katsina.
Maganar gaskiya, ci gaba da samun karuwar hare-haren ‘yanbindigar kan alumomin da ke a iyakar Kano, hakan ya nuna cewa, ya zma waji, a tashi ka’in da na’in, domin tunkarar kalubalen na rashin tsaron.
Shin me ya sa, yake zama wahala ga jami’an tsaro, tare da hadaka da gwamnatocin da ke a Arewa ta Yamma, suka gaza hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan na ‘yanbidiga da kuma aikata, suran manyan laifuka a jihohin?
A nan, za mu iya cewa, ga dukkan lamu, rashin yin hobbasan gwamnatocin da ke a wadannan jihohin na tunkarar matsalar ne, ya kara bai wa ‘yanbindigar karfin ci gaba da aikata, ta’asarsu, a jihohin.
Lokaci ya yi da gwamnatocin da ke a wadannan jihohin za su tashi kan jiki kan karfi, domin magance kai hare-haren da ke akuwa kan alumomin da ke zaune a iyakon su, musamman ta hanyar hada hannu da sauran hukumomin tsaro, domin a cimma wannan nasarar.
Bugu da kari, ya zama wajbi, gwamnatocin wadannan jihohin, su mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin alumomin su, daga hare-haren na ‘yan bindigar, wadanda har yanzu, suke ci gaba da cin Karensu, babu babbaka.
Kazalika, duba da yadda hare-haren na ‘yanbidagar ya durkusar da tattalin arzikin alumomin da ke a yankin, ya zama wajbi, gwamnatocin da ke a wadannan jihohin, su lalubo da mafita kan kalubalen na rashin tsaron.
Ra’ayin wannan Jaridar a nan shi ne, ya zama wajbi gwamnatocin da ke a wadannan jihohin, su tashi tsaye wajen, musamman duba da cewa, a yanzu, an shigo cikin kakar rani ne, wanda hakan zai sanya jami’an tsaro, da ke ci gaba da yakar ‘yanbindigar, samun damar kutsawa har zuwa sansanonin ‘yanbindigar domin ragargazarsu.
Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan zubar da mutuncin kasar da ‘yanbidigar ke ci gaba da yi, a idon duniya, musamman a yankunan da suka yi kaka gida.














