Dan wasan Kano Pillars, Yusuf Abdullahi, a ranar Lahadi, ya zazzaga kwallaye biyar a ragar kungiyar Gombe United a wasan gasar Firimiyar Nijeriya.
Wasan na 11 a jerin wasanni gasar ta 2023/2024, da aka buga a filin wasa na Pantami Township, Gombe, Kano Pillars ta lallasa kungiyar da ci 5-2, inda Abdullahi dan shekara 18 ya zura dukkan kwallayen biyar a raga.
- Manchester City Ta Koma Ta Uku A Teburin Firimiya Bayan Buga Canjaras Da Tottenham
- Yadda Gasar Firimiyar Bana Ta Shammaci Mutane
Yayin tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wasan, mai koyar da ‘yan wasan Kano Pillars, Abdullahi Maikaba, ya bayyana sakamakon wasan a matsayin mai armashi da burgewa.
Maikaba ya ce, ya yi matukar farin ciki da yadda daya daga cikin matasan ‘yan wasansa ya zura kwallaye biyar bayan kokarin da ya yi na zura kwallo a wasanni da suka gabata.
Sai dai, mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Gombe United, Mohammed Babaganaru, ya ki amincewa da bukatar tattaunawa da ‘yan jarida, inda ya ce “me kuke so in ce, me zan fada muku game da sakamakon wasan?”.