Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur kan yadda take sayarwa ga dillalai a tashar lodinsa (gantry) zuwa N1,350 kan kowacce lita, lamarin da ke nuna wani sabon ƙarin farashi a kasuwar man fetur ta Nijeriya.
Ƙarin farashin ya zo ne bayan kamfanin ya yi wasu ƙarin farashi a baya-bayan nan. A ƙarshen watan Agusta, Dangote ya ƙara farashin daga N1,200 zuwa N1,265 kan lita, bayan wasu ƙarin farashi da aka yi a watan Agustan 2026.
Sabon farashin na iya ƙara matsin lamba kan farashin da masu sayar da man fetur za su sayar a gidajen mai, saboda dillalai na iya ƙara farashin sayarwa domin biyan kuɗin da suke kashewa wajen sayen man daga matatar.
Matatar Dangote, wadda ke da ƙarfin tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a rana, ta zama muhimmiyar cibiyar samar da man fetur a Nijeriya. Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa matatar na ƙara samun ɗanyen mai daga Nijeriya domin ƙara yawan wanda take tacewa.
Ƙarin farashin ya kuma zo ne a daidai lokacin da Dangote ke shirin fara sayar da hannun jarin matatar ga jama’a ta hanyar IPO, wanda ake sa ran zai fara ne daga 14 ga Satumba zuwa 13 ga Oktoba 2026.













