ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

by Sulaiman
55 minutes ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba sabbin motocin aiki ga manyan makarantun gaba da sakandare da wasu hukumomin ilimi na jihar, a wani mataki da ya ce zai ƙara inganta ayyuka da tafiyar da harkokin ilimi.An gudanar da rabon motocin ne ranar Juma’a a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce motocin mallakar hukumomi ne, kuma za a yi amfani da su wajen gudanar da harkokin gudanarwa da ayyuka, sa ido kan ayyuka, tantance makarantu, halartar ayyukan hukuma da sauran nauyin da ya rataya kan cibiyoyin da suka amfana.Cibiyoyin da aka ware wa sabbin motocin sun haɗa da Jami’ar Tarayya ta Gusau, Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara, da Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau da ke Talata Mafara.

Zamfara

Sauran waɗanda suka amfana sun haɗa da Kwalejin Koyar da Aikin Jinya da Ungozoma ta Gusau, Hukumar Kula da Ayyukan Malamai, Hukumar Kula da Makarantun Sakandare, Sashen Tabbatar da Ingancin Ilimi, Kwalejin Nazarin Larabci da Shari’a ta Zamfara (ZACAS), da sauran cibiyoyin gwamnati na jihar.

ADVERTISEMENT

Da yake jawabi yayin rabon motocin, Gwamna Lawal ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara ƙwazo da ingancin ayyukan jami’an gwamnati, musamman ta hanyar samar musu da hanyoyin sufuri masu inganci da za su ba su damar gudanar da ayyukansu cikin sauri da sauƙi.

Gwamnan ya jaddada cewa motocin ba mallakar kowane jami’in gwamnati ba ne, sai dai dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne da aka bayar domin ayyukan hukuma.Ya ce, “Ya kamata a fahimci cewa waɗannan motocin ba wani haƙƙi ne na ƙashin kai da wani jami’in gwamnati zai mallaka ba. Dukiyoyin Gwamnatin Jihar Zamfara ne, kuma dole ne a yi amfani da su yadda ya kamata, musamman wajen gudanar da ayyukan hukuma kawai.

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

“Ina sa ran cibiyoyin da suka karɓi motocin za su ɗauki cikakken alhakin kula da su, yadda ake amfani da su, gyaransu da kuma adana bayanan da suka shafe su. Shugabannin cibiyoyin za su ɗauki alhakin duk wata ɓarna, amfani da su ba bisa ƙa’ida ba ko kuma lalacewar da za a iya kauce mata.

Zamfara

“Yayin da gwamnati ke ƙara zuba jari a fannin ilimi, dole ne mu gina al’adar kula da dukiyar gwamnati da ɗaukar alhaki. Ya kamata dukiyar jama’a ta ci gaba da amfani ga jama’a har tsawon lokacin da aka tanade ta.

“Dole ne mu himmatu wajen samar da ingantaccen tsarin gudanar da aiki, tare da ba da muhimmanci ga gaskiya, riƙon amana da ɗaukar alhaki.

“Gwamnatina za ta ci gaba da samar da gine-gine, kayan aiki da sauran tallafin da cibiyoyin ilimi ke buƙata domin inganta ilimin gaba da sakandare a Zamfara. A madadin haka, muna sa ran samun shugabanci nagari, gudanar da dukiya cikin taka-tsantsan, da kuma ingantattun sakamako a fannin karatu da gudanar da harkokin makarantu.”

Gwamna Lawal ya kuma taya cibiyoyin da suka amfana murna, tare da buƙatarsu da su tabbatar da cewa motocin sun amfani cibiyoyin, ɗalibai da al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya, maimakon amfani da su wajen biyan buƙatun wasu mutane na ƙashin kansu.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

MASU ALAKA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
Rahotonni

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari
Labarai

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari
Labarai

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Next Post
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.