• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussan Da ‘Yan Siyasa Za Su Koya A Zaben 2023

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
Siyasa

Sannu bata hana zuwa sai dai  dade ba a je ba haka dai  masu iya magana suke cewa hakika an dade ba a je ba,amma daga karshe dai an je maganar zabubbykan da aka yi tsakanin 25 ga Fabrairu da 18 Maris 2023,da sun shafi na Shugaban kasa ‘yan majalisun kasa.

Bayan kammala su ne sai zaben gwamnoni da ‘yanmajalisun Jihohi da aka kammala ranar Asabar ta makon daya gabata,masu yin murna saboda sun yi nasara sun yi,wadanda kuma suke  bakin-ciki ba domin komai ba sai saboda basu samu nasara ba.

  • A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d
  • Manoman Rani Na Sa Ran Samar Da Shinkafa Da Alkama Mai Yawa A Taraba

Haka ne al’amarin rayuwa yake musamman ma duk abinda aka riga aka sa ma ranar yin shi ko ba dade-ko ba jima sai shi da ranar sun hadu,kamar yadda su ranakun zaben suka zo suka bar wasu cikin mamaki,to mamaki mana domin kuwa abubuwan da ba a tsammani suka faru inda Giwa tayi tuntube ta kuma Kare.Idan dai ba ayi saurin mantawar ba ko shakka babu Giwar tayi tuntuben ta Kare.Abubuwa da yawa sun faru wadanda idan aka bi su sau da kafa za a iya ganewa gaskiya mnayan darussa ne da suka faru wasu sun kasance wata manuniya ce su ‘yan siyasar yadda zasu fuskanci zabubbukan suka kasa ganewa.

Kafin dai a kai ga yin su zabubbukan na shekarar 2023 abin ya fara kasancewa wani abu ne da masu iya magana ke cewa “Kukan Kurciya Jawabi Ne Mai Hankali Ke Ganewa” wato ita maganar kungiyar gwamnonin nan na sassan Kudu maso Kudu,Kudu maso gabas,kudu maso yamma,sai kuma Arewa ta tsakiya, da aka fi sani da G5 data hada da gwamnonin jam’iyyar PDP biyar wadanda aka fi sani da sunan, sai ga shi uku daga cikinsu basu samu biyan bukatar ba domin sun kasa lashe zaben Sanatan  da  aka yi tare dana Shugaban kasa a kokarinsu na su tafi hanyar yin ritaya daga karshe a harkokin siyasa idan ba wata bace Allah ya bullo da ita cikin rashin sanin masu kokarin zuwa majalisar Dattawa ta kasa.Wannan bayan sun kammala wa’adinsu na shekaru takwas na hudu sau biyu.

Kungiyar G5 ta kunshi gwamnonin PDP  biyar Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu), Samuel Ortom (Benuwe), Seyi Makinde (Oyo) da kuma Nyesom Wike  na(Ribas).Gwamnonin biyar sun kulla kawancen ko kuma abokantakar  ce, sai bayan da aka kammala zaben fidda –gwani na Jam’iyyar PDP a watan Mayu 2022 inda suka nemi Shugaban jam’iyyar na kasa Sanata, Iyorchia Ayu cewa ya sauka daga mukaminsa domin ya bar ma wani daga sashen Kudu da zai maye makwafinsa.Wannan kuma wata shawara ce da suka ba dan takarar jam’iyyar  PDP idan ya amince da ita  su zasu ba shi goyon baya lokacin zaben Shugaban kasa na 25 ga Fabrairu

LABARAI MASU NASABA

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

Duk Atiku Ayu suka kira wannan ikirarin gwamnonin biyar a matsayin wani wasan yara ne inda suka yi watsi da bukatar tasu ta cewa sai Sanata Ayu ya sauka sannan su marawa Atiku Abubakar baya lokacin zabe.

Kamar sanin kowa ne lokacin zaben Shugaban kasa Atiku Abubakar bai samu nasara ba a duk Jihohin biyar, Atiku,Peter Obi jam’iyyar Labour Party  ya samu nasara a Jihohin Enugu Abia, Bola Tinubu  na APC ya samu nasara a Jihohin Oyo, Benuwe, da  Ribas.

Daga cikin  ‘yan kungiyar ta G5,Ortom, Ikpeazu, Ugwuanyi da Wike  duk gwamnoni ne masu kammala wa’adinsu na shekaru hudu sau biyu yayin da shi Makinde shi shekara hudu ne yake gab da kammalawa ya tsaya yana neman a sake zaben sa karo na biyu wanda yayi sa’a zai sake komawa gidan gwamnati ya sake maimaita wasu shekaru hudun.An sha yin tarurruka da suka fi shurin masaki saboda sasanta manyan gaggan mutanen biyu Atiku Abubakar da Nyesom Wike amma abin yaci tura,wani abin mamaki ma shi gwamnan yafi kowa tsiwa wanda ke bi ma shi baya shine na Benuwe. Daga karshe shi dama Shugaban jam’iyyar PDP na kasa ko a Jihar ta shi ta Benuwe ba wani abu bane domin sun kasa rufa masa asuri bare shi ma ya rufa ma wani.

Shi yasa Hausawa lalle sun kyauta da suka ce “Kowa Yace Ruwan Wani Ba Zai Tafasa BaTo Shi Nashi Ko Dumi Ba Ya Yi” Shi Wike bai nemi wata dama ta tsaya takarar Sanata ba amma ya san irin tuggun  siyasa na ‘yan siyasa daya shirya saboda kuwa ai bayan zaben Shugaban kasa dana ‘yan majalisun kasa, jam’iyyarAPC har godiya ta  yi ma shi kan irin gudunmawar daya bata,hakanan ma gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom da bakinsa ya furta cewa da ace shi ba dan jam’iyyar  PDP bane da ya zabi Peter Obi ashe dama manufarsa ce yake fada saboda ai lokacin zaben Shugaban kasa dan takarar na  APC ne ya lashe zaben Shugaban kasa da gaggarumar nasara  a Jihar da kuri’u 310,468 Peter Obi  ya samu 308,372 Atiku Abubakar dantakarar  PDP ne ya zama na uku da 130,081 yayin da Kwankwaso yake da 4,740.Idan da ace sun yi PDP zallah sai ya samu kuri’u fiye da  700,000 in babu tuggun ‘yan siyasa domin kuwa ai Jiha ce ta Shugaban jam’iyyar PDP na kasa amma sai ga dantakararta ya zo na uku.Hakika an yi amfani ne da addini da kabilanci matuka a zabubbukan Shugaban kasa dana majalisun kasa idan ba haka ba ai babu yadda za ayi wani dantakarar Shugaban kasa daga sashen Kudu maso gabas har ya shigo Arewa yayi ma ‘yan takarar  na Arewa raga-raga abu ne daure kai ma a Arewa ta tsakiya,wannan ba karamin darasi bane kowanne dan siyasa wala babba ko matashi  ya dace ya yi  koyi da shi zuwa gaba.

Ba abu bane mai kyau ga dan siyasa ya rika kurin cewa shi dole ne ko wanne lokace shi zai cigaba da damawa ko damawa da shi, yin hakan bai yi ma kan shi adalci ba ko kadan,dalili kuwa  rami ne ya gina bai san shi ne zai fada ba amma sai ya samu kan shi a ciki,ba kuma wanda zai taimaka wajen dauko shi ya shiga ke nan Shi yasa maraigayi Alhaji Mamman Shata Katsina a wakarsa mai taken “A Gargadi Mai Gina Ramin Mugunta” yace ‘ya kai mai gina ramin mugunta to ka gina daidai kwaurinka watakila kai zaka fada”,amma yawancin masu irin hakan wani wawakeken rami ne mai zurfi suke ginawa wanda duk ya fada gaba daya zai iya shanye shi kamar dai yadda ya faru ga wasu manyan ‘yan siyasa da suka mayar da majalisun Jihohi dana kasa kamar kayan gadonsu ko kuma mallakin kansu.Irin sune suka gina wa kansu ramin muguntar wadda  mawaki ya yi gargadin kada su gina shi, maimakon su rika jawo su matasa suna koya masu ga yadda dabarun siyasa suke sannu a hankali sai su koya har watarana suma su fara nuna gwanintarsu,sai ta kasance su ba hakan suke so ba.Ko dai ba magana a zura ido ta ishi mai hankali kamar yadda marigayi Sani Sabulu Kanoma ya fada a wakarsa inda yace, “ In ba a jiran lokaci akwai wahala can gaba’ yace “Na san dan Adam watarana dan Adam halin agaza aggarai,shi zai ishe ka a gida yace maka taso mu je sai kun fara tafiya yace maka ya gaji”.

Wasu ‘yan siyasa anasu ganin ko yaushe su kasance sune na BARA SUNE NA BANA SUNE NA SHEKARAR BASHASHA bayan kuwa al’amarin ai sam ba haka yake ba,Allah shi ne mai kowa mai komai mai yin abinsa inda yaso da lokacin da yaso ya kasance an so abin,dole sai kowa ya jira lokacinsa duk kuma tagumin mutum ai baya wuce habarsa.Idan kuma kai yana da tsoka kamata yayi kowa ya taba na shi ya ji.Daga karshe duk wata turjiyar da za ayi yadda yaso haka abin zai kasance.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Next Post
Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle

Shinge 4 Da Sabon Gwamnan Zamfara Ya Tsallake Kafin Ya Doke Matawalle

LABARAI MASU NASABA

NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.