A yau Alhamis, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya gabatar da jawabi a bikin kaddamar da bikin baje kolin cinikayyar fasahohin zamani na duniya karo na biyar a birnin Hangzhou, da ke lardin Zhejiang na kasar Sin.
Ya bayyana cewa, ya kamata al’ummomin duniya su karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tsaowa da masu ci gaba a fannin cinikayyar fasahohin zamani, tare da samar da karin tallafi ga kasashe masu tasowa ta fuskar fasaha, da kayayyakin more rayuwa, da kuma horar da ma’aikata.
Li ya kuma bayyana cewa, a tsawon shekaru da dama, kasar Sin tana ci gaba da yin tsayin daka wajen karfafa batun dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Kuma a wannan zamani na fasahohi, kasar za ta ci gaba da rungumar duniya, da zurfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya tare da dukkan bangarori, da kuma karfafa farfado da tattalin arzikin duniya da bunkasa shi cikin hadin gwiwa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














