ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NAPTIP Ta Buƙaci ‘Yan Jarida Su Ƙara Bincike Wajen Bayar Da Rahotannin Cin Zarafin Mata

by Shehu Yahaya
6 days ago
NAPTIP

Hukumar yaƙi da safarar mutane ta ƙasa (NAPTIP) da ƙungiyar International IDEA sun buƙaci ‘yan jarida su ƙara zurfafa bincike da wayar da kan al’umma domin yaƙi da cin zarafin mata da sauran nau’o’in cin zarafi ta fuskar jinsi (SGBV) a Nijeriya.

Sun yi wannan kiran ne yayin wani taron karawa Juna ilimi ga ‘yan jarida masu yaƙi da cin zarafin mata da jinsi (SGBV Media Corps) a jihar Kaduna.

Taron ya haɗa wakilan hukumar NAPTIP da International IDEA da ƙwararrun ‘yan jarida domin tattauna hanyoyin dakile cin zarafi tare da kare masu rauni a cikin al’umma domin tabbatar da ɗaukar matakin da ya dace kan masu aikata laifukan.

ADVERTISEMENT

Da yake magana a madadin Darakta-Janar na NAPTIP, shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Vincent Adekoye, ya buƙaci ‘yan jarida su ƙara himma wajen wayar da kan jama’a tare da sanya ido kan masu aikata laifukan cin zarafi.

Adekoye ya ce masu aikata irin waɗannan laifuka na ci gaba da ƙirƙirar sabbin hanyoyi wajen gudanar da ayyukansu, lamarin da ya sa ake buƙatar ‘yan jarida su kasance masu lura da kuma zurfafa bincike kan duk wani lamari da ya shafi cin zarafi.

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai za su iya takawa wajen kare yara, matasan da ke rayuwa a kan tituna da mata daga cin zarafi da amfani da su ta haramtacciyar hanya.

Jami’in ya kuma bukaci ‘yan jarida su fahimci dokokin da suka shafi cin zarafin mata da sauran laifukan da suka shafi jinsi, tare da amfani da kafafen yaɗa labaransu wajen fallasa laifuka, wayar da kan jama’a da kuma ci gaba da jan hankalin al’umma kan matsalar.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki su riƙa bibiyar manufofin gwamnati, tantance matakan da hukumomi ke ɗauka da kuma tabbatar da cewa an ɗora wa waɗanda abin ya shafa alhakin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cewarsa, shirin na tsawon shekaru huɗu an tsara shi ne domin taimakawa wajen kawar da cin zarafin mata da sauran nau’o’in cin zarafi ta fuskar jinsi a Najeriya, ta hanyar ci gaba da wayar da kan jama’a da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Ya bayyana cewa ingantaccen aikin jarida zai taimaka wajen ƙara fahimtar al’umma kan matsalar, ƙarfafa gwiwar waɗanda aka zalunta su kai rahoton abin da ya faru da su, tare da inganta ɗaukar mataki kan masu aikata laifukan.

A nata jawabin, mai Kula da jagoranci ‘yan jarida masu yaƙi da cin zarafin mata da jinsi a jihar Kaduna, Dakta Lauratu Abdulsalam, ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta yadda ake bayar da rahotannin irin waɗannan laifuka.

Ta ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin da abin ya shafa zai taimaka wajen wayar da kan jama’a, inganta bayar da rahotanni cikin kwarewa da kuma ƙarfafa ƙoƙarin dakile cin zarafi.

Ta ƙara da cewa ya kamata ‘yan jarida su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin kwarewa da sanin ya kamata, musamman wajen kare mutuncin waɗanda aka zalunta da kuma tabbatar da cewa rahotanninsu suna taimakawa wajen samar da mafita.

NAPTIP
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak Bayan Tsare Ta A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Majalisar Malamai Ta Ƙasa Ta Buƙaci Gwamnati Ta Yi Wa El-Rufai Da Sheikh Sani Zaria Adalci
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Kwalejin Koyar Da Ƙwararrun Ma’aikatan Jinya A Rigasa
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    2027: Kaddamar da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna Alamar Nasarar Tinubu Ce A 2027 —Kakakin APC

MASU ALAKA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya
Labarai

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Next Post
’Yan Adawa Za Su Iya Fitar Da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Kwanaki Kaɗan Kafin Zaɓen 2027 – Lukman

’Yan Adawa Za Su Iya Fitar Da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Kwanaki Kaɗan Kafin Zaɓen 2027 - Lukman

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.