Fusatattun matasa a garin Gwashi da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara sun tare ayarin motocin Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Malam Mummuni, tare da yi masa ƙawanya a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, 2026. Lamarin ya auku ne a yayin da mataimakin gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya garin biyo bayan harin ƴan bindiga da ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro tara da fararen-hula da dama kwanaki kaɗan da suka gabata.
Bayanai sun nuna cewa matasan sun toshe manyan hanyoyin shiga garin suna cewa “Ba ma yi”, sakamakon zargin gwamnatin jihar da yin watsi da su a lokacin da ƴan bindiga suka addabi yankin. Mazauna garin sun bayyana cewa ba wani jami’in gwamnati da ya zo jajanta musu a lokacin da suke zaman makoki, sai bayan kwanaki da lamarin ya lafa, lamarin da ya fusata matasa suka riƙa jifan ayarin motocin gwamnan.
Tsananin tashin hankalin ya tilasta wa mataimakin gwamnan da tawagar jami’an tsaronsa neman maɓoya a cikin gari domin tsira daga harin fusatattun matasan.
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, ƙungiyoyin al’umma sun bayyana cewa matakin na nuni da yadda al’ummar Bukkuyum suka kai maƙura wajen jin haushin matsalar rashin tsaro, inda suka shafe kusan mako guda ba sa iya fita zuwa gonaki ko neman abinci sakamakon tsoron ƴan bindiga da kuma rashin ababen more rayuwa a yankin.
Har yanzu ba mu samu labarin ko mataimakin gwamnan da tawagarsa sun samu fitowa daga cikin garin Gwashi ba, sakamakon suna jiran isar ƙarin dakarun soji da ƴansanda domin ba su kariya don ficewa daga garin cikin kwanciyar hankali.
Wannan tirjiya ta sake fito da ƙalubalen rashin tsaro da kuma tsananin ɓacin ran da al’ummomin karkara a Jihar Zamfara ke ciki kan abin da suka kira rashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki daga gwamnati wajen kare rayukansu.














