ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tun Wuri Ka Bayyana Goyon Bayanka Ga APC Idan Manufarku Ɗaya – ADC Ga Kwankwaso

by Abubakar Sulaiman
5 days ago

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar ADC ya mayar da zazzafan martani ga ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya buƙace shi da ya fito fili ya bayyana komawarsa Jam’iyyar APC mai mulki a idan har yana tare da manufofinta.

Wannan martani na zuwa ne a Abuja biyo bayan kalaman da Kwankwaso ya yi a daren Lahadi, inda ya zargi ADC da ƙulla maƙarƙashiyar ruɗar da al’umma cewa tikitinsu na NDC zai janye wa Alhaji Atiku Abubakar a babban zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da kwamitin kamfen ɗin na Atiku ya fitar, ya zargi Kwankwaso da zama ɗan amshin-shatan jam’iyya mai mulki da ke aiki a ɓoye domin raba ƙuri’un ƴan adawa domin APC ta samu nasara.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta bayyana cewa duk wani ɗan adawa na gaskiya ya kamata ya rungumi haɗin kai domin ceto ƴan Nijeriya daga matsin tattalin arziƙi da rashin tsaron da gwamnatin Tinubu ta jefa ƙasar a ciki, maimakon nuna son kai da ƙaddamar da hare-hare kan sauran ƴan adawa.

Haka kuma, kwamitin ya ƙalubalanci Kwankwaso da ya daina yaudarar magoya bayansa da sunan ɗan adawa a ƙarƙashin NDC, yana mai nuni da cewa yadda yake mayar da hankali wajen sukar Atiku Abubakar maimakon gwamnati mai ci babbar shaida ce da ke nuna ainihin inda biyayyarsa take.

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

Sun jaddada cewa tikitin takarar Atiku zai ci gaba da mayar da hankali kan bayyana hanyoyin magance tsadar rayuwa, rashin tsaro, da rashin aikin yi, ba tare da ɓata lokaci kan abin da suka kira dabarun raba kawuna ba.

Wannan sabuwar cacar-baki tsakanin manyan jam’iyyun adawar biyu na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Nijeriya ke nuna damuwa kan yadda rarrabuwar kawunan ƴan adawa ka iya sake buɗe wa APC hanyar samun nasara a 2027.

Duk da wannan taƙaddama, kwamitin yaƙin neman zaɓen na ADC ya buƙaci ƴan ƙasa masu buƙatar canji na gaskiya da su haɗa kai a ƙarƙashin inuwar takarar Atiku Abubakar a matsayin mafita mafi inganci ga ƙasar.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh
  • Abubakar Sulaiman
    Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
  • Abubakar Sulaiman
    Aikin Titin Jirgin Ƙasa Na Kaduna Zuwa Kano Ya Kai Kashi 90%

MASU ALAKA

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’
Siyasa

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026
Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo
Siyasa

Ku Yi Duk Abin Da Za Ku Yi Domin Ganin Tinubu Ya Ci Zaɓe – Tompolo

October 22, 2026
Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027
Siyasa

Wike Ya Buƙaci ’Yan Jam’iyyar PDP A Abuja Su Goyi Bayan Tinubu da ’Yan Takarar APC A 2027

October 22, 2026
Next Post
Fadar Shugaban Ƙasa Da Gwamna Makinde Sun Shiga Taƙaddama Kan Rabon Ribar Biliyan 250 Ta NLNG

Fadar Shugaban Ƙasa Da Gwamna Makinde Sun Shiga Taƙaddama Kan Rabon Ribar Biliyan 250 Ta NLNG

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.