Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa tabbatar da dimokuradiyya a Nijeriya.
Sannan gwamnan ya taya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa nasarar da ya samu na zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2023. Kamar yadda kwamishinan yada labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya shaida wa manema labarai a Kano.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin takardar jawabin taya murna wanda ya rattabawa hannu da kansa, Gwamnan ya ce, nasarar Tinubu na zama wanda zai yi wa jam’iyyar APC takara a 2023, domin dorawa kan ayyukan raya kasa da Shugaban Buhari ya fara.
Ya ce Jagaban ya cancanci samar da ingantaccen jagorancin da ake bukata wanda zai tabbatar da kara jajircewa wajen gina kasar nan a tafarkin dimokuradiyya.
Hakazalika, Gwamna Ganduje ya jinjina wa kokarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa bayar da kyakkyawar damar tsayar da jajirtaccen da zai yi wa jam’iyyar APC takara da kuma samun nasarar ta hanyar da yadda jam’iyyar ta bi wajen gudanar da zaben fid da gwani.
Gwamnan ya bukaci sauran ‘yan takarar su hada kai hada kai wajen gabin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaben 2023 domin tabbatar da cikakkiyar dimokuradiyya.
Haka kuma ya bukaci Tinubu a matsayinsa na jagora ya yi amfani da kwarewarsa da fahimtarsa ga tattalin arzikin kasa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023.