A daidai lokacin da al’ummar duniya ke bikin ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara , ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don tattaunawa da tafakkuri a kan irin gudmmawar da mata suke bayar wa a fagen bunkasa rayuwar al’umnma daban-daban, tare da kuma karfafa mata wajen jajircewa da kokari a dukkan fagen rayuywar da suka samu kansu don baje kolin baiwar da Allah ya basu ta hazaka.
A wannan nahiya tamu an samu mata da suka nuna bajinta a fannonin rayuwa masu yawa, idan zamu koma ga tarihi a nan yankin Arewacin Nijeriya, zamu iya tunawa da Sarauniyar lardin Zazzau, wato Sarauniya Amina, wadda ta jagoranci masarautar Zazzau zuwa bunkasar da aka dade ba a samu irinta ba. Ta jagoranci dakarun jarumai mazaje a fagen yaki da dama inda aka samu nasarar fadada masarautar Zazzau zuwa matsayin da take a halin yanzu.
Idan kuma muka yi dubi ga tarihi na baya bayan nan zamu ga irin yadda mata irinsu Hajiya Gambo Sawaba ta yi fice wajen nemawa al’umma ‘yanci a lokacin harkokin siyasar jamhoriyya ta daya da ta biyu. Hajiya Gambo Sawaba ta zama samful ga mata na nuna cewa, duk abin da namiji zai yi to mata ma za su iya matukar aka basu cikakkiyar damar cimma burinsu na rayuwa. Muna iya tabbatar da wannan lamari ne in muka lura da irin gudunmawar da Hajiya Hadiza Bala Usman ta bayar a bangarori da daban-daban na rayuwar al’umma a ‘yan shekarun nan musamman in aka lura da gudunmwar da ta bayar wajen bunkasa rayuwar matan karkara ta hanyar samar masu da sana’o’in dogaro da kai. Ta kuma kasance a kan gaba a wajen fafutukar neman a kubutar da ‘yan matan nan a makarantar Chibok da ke Jihar Borno wadanda ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace, fafutukar da aka yi wa lakabi da #BringBackOurGirls.
A saboda haka a daidai wannan lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya ta wannan shekarar, Hajiya Hadiza Bala Usman na daya daga cikin matan da jaridar LEADERSHIP HAUSA za ta sa a gaba don nazari tare da daukar darussan da za su amfani musamman ‘yanmata masu tasowa, domin kuwa ta yi rawar gani a mukaman da ta rike daban-daban a sassan kasar na harma da kasashen waje.
Ita dai Hajiya Hadiza Bala Usman, an haife ta ne a garin Zariya da ke Jihar Kaduna a ranar 2 ga watan Janairu na shekarar 1976, ta yi karantunta na sakandire a Gobernmant Day Secondary Samaru Zariya daga na ta zarce Jami’ar Ahmadu Bello Zariya inda ta samu digiri a fannin harkokin kasuwanci wato (Bachelor’s Degree (B.Sc.) in Business Administration) daga nan ta samu nasarar zuwa kasar Ingila inda ta yi digirinta na biyu a Jami’ar ‘Unibersity of Leeds’.
Hajiya Hadiza Bala Usman ce mace ta farko da ta taba shugabantar Hukumar Kula da Tashoshin Ruwan Nijeriya, NPA a lokacijn da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin Shugaban hukumar na NPA a watan Yuli na shekarar 2016, kafin nan ta rike mukamin shugabar ma’aikatan ofishin gwamnan Jihar Kaduna wanda nan ma ita ce mace ta faro da ta taba rike irin mukamin a yankin rewacin Nijeriya gaba daya.
A tarihin rayuwarta na aiki, wanda ta yi a tsakanin hukumomn gwamnati da bangaren hukumomi masu zaman kansu, ta fara da aiki ne a hukumar kula da sayar da hannun jarin kamfanonin Nijeriya wato ‘Bureau of Public Enterprise [BPE]’, hukmar ce aka dora wa alhakin sayar da hannun jarin kamfanonin tarayyar Nijeriya, ta gudanar da aikinta a wannna ma’aikata yadda ya kamata kuma a cikin nasara.
Ganin irin nasarar da ta samu a aikin da aka damka mata a hukumar BPE ne ya sanya Hukumar Bukasa Kasashen Duniya ta Majalsiar dinkin Duniya (UNDP) ta dauketa aiki a mastayin mataimakkiya na musamman mai kula da ayyuka a ofishin Ministan yankin babban birnin tarayya Abuja a tsakanin shekarar 2024 zuwa shekarar 2008 daga nan ne ta yi aiki a wata kungiya mai zaman kanta, sai kuma zama mataimakiya ta musamman ga Ministan Abuja a bangaren aiwatar da ayyuka daga watan Oktoba na shekarar 2004 zuwa watan Janairu na shekarar 2008, daga nan ta yi aiki tare da kungiya mai zaman kanta NGO mai fafutukar gudanar da sahihin harkokin mulki a Abuja a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
A matsayin martani a kan yadda aka sace ‘yan mata 219 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi daga makarantar sakandiren ‘yan mata na garin Chibok da ke Jihar Borno yankin Arewa maso gabashin Nijeriya da aka yi a watan Afrilun shekarar 2014 kuma musamman ganin yadda ta dauki karatun mata da matukar muhimmanci ganin karatunn mata yana koma baya a yankin arewa, Hajiya Hadiza da sauran mnasu fafutuka suka kafa kungiyar nan da ta rika shirya gangami da zaman dirshan a Abuja wadda aka yi wa lakabi da #BringBackOurGirls, kungiyar ta kasance a kan gaba wajen kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen ganin an ceto ‘yan matan, ta kuma ci gaba da wannan fafutuka har zuwa lokacin da ta zama shugabar NPA ta kuma ci gaba da kasancewa tare da ‘yan kungiyar ko a lokacion da take a matsayin shugabar NPA, don a duk sadda ka ganta a wajen taruka zaka ganta da bajin da ke alamta neman a ceto ‘yan matan na Chibok.
A watan Agusta na shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Hajiya Hadiza Bala Usman a matsayin manba a Kwamintin nan na Farfesa Itse Sagay wadda aka dora wa alhakin yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya a nan ma ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.
A matsayinta na ‘yan jam’iyyar APC, Hajiya Hadiza Bala Usman ta yi wa jam’iyyar aiki a matakji daban-daban ta kuma nuna bajinta da kwarewa a dukkan mukaman da ta rike wannan ya jawo mata soyayya da mutumci da amincewa daga mafi yawan shugabanin jami’iyyar, cikin mukaman da Hajiya Hadiza ta rike sun hada da:
Mamba a kwamitin jam’iyyar APC da ta tsara manufofi da kudurorin jam’iyyar a tsakanin watan Janairu na shekarar 2014 zuwa watan Disamba na shekarar 2014, ta kuma zama mamba da kuma sakatariyar kwamitin tsara harkokin zabe na jam’iyyar APC a tsakanin watan Yuni na shekarar 2014 zuwa watan Afrilu na shekarar 2015. Kwamitin ne ta tsara dabarun da jam’iyyar ta yi amfani da su wajen lashe zaben da aka gudanar.
Ta kuma zama sakatariyar kungiyar gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a tsakanin watan Janairu na shekarar 2015 zuwa watan Afrilu na shekarar 2015. Haka kuma Hajya Hadiza ta kasance mamba a kwamitin tsara yadda za a kafa sabuwa gwamnati a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Mayu na shekarar 2015. Ta kuma zama mamba a kwamitin tsara taron zaban shugabanninjam’iyyar APC.
Cikin mukaman da Hajiiya Hadiza ta rike sun kuma hada da mamba kuma sakatariyar kwamitin da ya jagoranci yadda aka zabo wa jam’iyyar dan takarar shugabancin kasa a shekarar 2019.
Saboda jajircewar ta da aiki tukuru, Hajiya Hadiza Bala Usman ta sanu lambobin yabo da dama a ciki da wajen kasar nan, ita ce ta lashe lambar zama wadda ta fi tasiri a cikin matan Nijeriya a shekarar 2014, kamar yadda jaridar ‘Financial Times [FT]’ ta fitar, gidan talabijin na CNN ya kuma zabe ta a cikin mata bakaken fata dari da suka fi tasiri a duniya a shekarar 2014, haka kuma mujallar Ebony ta zabe ta a mastayin daya daga cikin mata 100 da suka fi tasiri a duniya a shekarar 2014, a shekarar 2018 kuma an zabe ta a mastayin daya daga cikin mutanen da suka fi mutunci a Afrika, ‘African Descent (MIPAD)’ Shirin na daga ciki wani tsari don tallafa wa shirin majalisar dinkin duniya na bikin ranar al’umma da ke da asali daga Afrika.
Bayani ya nuna cewa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta samu karramawa daga wata mujallar kasuwanci mai suna BUSINESSDAY, mujallar kasuwanci mafi tasiri a Nijeriya, an karramata ne a ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2017 daga nan kuma kamfanin watsa labarai na ‘DAAR Communications’ ya karrama Hajiya Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar da ta ke gudanar da harkokin ma’aikatarta ba tare da munamuna ba, wannan kuma yana da nasaba da yadda ta samar da tsare-tsare masu muhimmanci da suka kai ga bunkasa yadda ake tafiyar da harkokin hukumar tashar jiragen ruwa ta Nijeriya NPA, wanda hakan ya kara saar da hanyoyin kudin shiga da jawo masu zuba jari daga ciki da wajen kasar nan. Haka kuma a lokacin da take shugabanci NPA ta rike mukamin mataimakiyar shugabar hukuma kungiyar tashohshn jiragen ruwa ta duniya.
Tarihi ya kuma nuna cewa, ba a taba samun ci gaban da aka samu ba a NPA kamar lokacin da Hajiya Hadiza ke shugabantar hukumar tun da aka kafa hukumar fiye da shekara 63 da suka wuce
A ranar Lahadi 11 ga watan Disamba 2022 ne Kungiyar Tuntuba ta yankin Funtuwa a Jihar Kaduna, kungiyar da aka fi sani da (Funtua Consultatibe Forum) ta gudanar da taron na shekara-shekara inda ta karrama wasu fittatun ‘yan asalin jihar tare da kaddamar da Mujallar kungiyar mai suna ‘The Trumpet Magazine’, taron ya gudana ne a karkashin jagorancin Farfesa Abdulmunin Ibrahim.
Cikin wadanda aka karramar sun hada da Hajiya Hadiza Bala Usman, sun bayyana cewa, sun karrama ta ne saboda irin yadda ta bayar da gudummawa wajen bunkasa rayuwar mata da yara kanana a fannoni da dama, shugaban kungiyar, Dakta Zaharadeen Idris ne ya bayana irin ayyukan da Hajiya Hadiza ta yi wadanda suka amfani al’ummar Jihar Katsina.
Shugaban kungiyar ya kuma bayyana cewa, sun gayyaci tsohuwar shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ne don ta jagoranci kaddamar da Mujallar su saboda yadda ta nuna kishin Jihar Katsina a lokacin da take a kan karagar shugabancin NPA. Ya ce, ta samar da ayyukan cigaba da bunkasa rayuwar al’umma da dama a yankuna mazabun majalisar dattawa uku da ke a Jihar Katsina, ayyukan kuma sun hada da horar da matasa sana’oin dogaro da kai a garin Dangani na karamar hukumar Musawa, horas da mata hanyoyin tsaftace muhalli a garin Daura, samar da fittilun kan titi masu amfani da hasken rana a yankuna kananan hukumomin Musawa, Mutazu, Malumfashi, Kafur da Bakori haka an samar da irin wannan fitillun kan titi masu amfani da hasken rana na kananan hukumkomin Danja, Funtua, Kankara, Sabuwa da kuma Faskari.
Bayani ya kuma nuna cewa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta dauki nauyin horas da mata da matasa sana’oin dogaro da kai a kananan hukumomin Dandume da Funtua.
A bangaren ilimi kuwa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta gina tare da yi wa wasu makarantu a sassan jihar Katsina kwaskwarima, wananna aiki ya shafi kusan dukkan kananan hukumomin Jihar gaba daya da kuma gyara asibitin masu fama da cutar yoyon fitsari da ke garin Babban Ruga ta Jihar Katsina.
Dakta Zaharadeen Idris ya kuma tabbatar da cewa, Hadiza Bala Usman ta yi wadannan ayyuka kuma ga wannan yake son ganin su yana iya zuwa garuruwan da aka zayyana don ya gane wa kansa, a kan haka ne kuma ya yi kra ga ‘yan asalin Jihar Katsina da suke rike da madafun iko a hukumomi da kamfanonin gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya su jajirce wajen koyi da Hajiya Hadiza ta hanyar samar da ayyukan cigaban ga al’umma Jihar.
Idan za a iya tunawa, Hajiya Hadiza Bala Usman da kanta ta jagoranci tawagar shugabanin gudanarwar NPA zuwa kai gudummwar tallafin kayan abinci ga ‘yan gudun hijirar da yakin Boko Haram ya tarwatsa a sansanin su da ke Jihar Borno inda gwamnan jihar na lokacin kuma zababben mataimakin shugaban kasa a halin yanzu, Sanata Kassim Shettima ya karbi tallafin a madadin ‘yan gudun hijirar, ya yaba da kokarinta a kan yadda take tunawa da marasa galihu da mutanen da ke cikin matsala a sassan kasar nan.
Wannan kokari na Hajiya Hadiza ba wai ya tsaya a bangaren arewacin Nijeriya kawai ba ne, don kuwa al’ummar Bundu-Ama na karamar hukumar Fatakwal da kuma al’ummar Okari-Ama na karamar hukumar Okrika da ke Jihar Ribas sun samu tallafi na musamman don bunkasa kananan sana’o’insu, kayan da suka samu sun hada da Firiza 35, Injinan nika 80 da Injinan walda 40.
A jawabinta yayin mika kayan tallafin, Hajiya Hadiza ta ce, ana fatan wadanna kayan zai taimaka wajen bunkasa sana’o’in al’umma yankin, musamman mata ta yadda za su samu dogaro da kansu.
Haka kuma irin wannan tallafin da taimako na tausayawa da Hadiza Bala Usman ke bayarwa ya isa makarantar firamare na Sheik Abubakar Gumi da ke ungwar Tudun Wada, ta Jihar Kaduna, inda aka gabatar musu da kujerun zama dana karatu, an yi haka ne ,in ji ta don a kara karafafa harkar karatu a tsakanin yaran makarantan, wani babban manaja a NPA, Alhaji Aliyu Nakamba, ya wakilce ta a wajen bayar da tallafin, ya ce, an samar da tebura da kujeru fiye da 300 da kuma kujeru da tebura na malamai fiye da 20.
Wannan tallafin zai taimakawa gwammantin jihar Kaduna zai kuma karfafa wa yara da malaman makarantar samun yanayin ma kyau na gabatar da koyawar da kuma daukar darasi gaba daya.
Wannan kokari na Hajiya Hadiza Bala Usman ya nuna irin yadda take son ganin an inganta yanayin samun ilimin yara kanana musamman mata, wanda hakan ya yi daidai da kiraye kirayen majalisar dinkin duniya na samar wa mata yanayin da zai kai ga bunkasar su a dukkan fanonin rayuwa ba tare da nuna musu bambanci ba.
A kokarinta kuma na inganta ilimin kimiyya da fasaha a jami’o’in kasar nan, Hajya Hadiza Bala Usman ta bayar da tallafin ginannen dakin karatu na zamani wadanda aka kawata da na’u’rar kwamfuta ‘e-library’ ga jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi, inda aka samar da kwamfufuta 40 don amfanin daliban makarantar.
Babban jami’i a NPA, Tukur Buba ne ya jagoranci tawagar da ta kai tallafin a madadin hukumar gudanbarwa, ya kuma ce an yi haka e don a kara bunkasa ilimin kimiyya da fasaha ga daliba tare da kuma tabbatar da sun samu nasara a harkokin karatunsu.
A wannan karo na siyasa 2023 da muke ciki, wanda ya kai ga samun nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban Nijeriya a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu 2023, Hajiya Hadiza Bala Usman ta bayar da gaggarumin gudummawa tun daga yadda ta tattaro kan magoya bayan jam’iyyar na Jihar Kaduna da Katsina da yadda ta tsayu wajen ganin an samu nasarar.
Tabbas a daidai wannan lokaci da muke bikin ranar mata ta duniya kamar yadda majalisar dinkin duniya ta ware, dole mu yi jinjina ga mata irin su Hadiza Bala Usman, wadda ta tsayu wajen ganin mata a fadin Nijeriya sun sama rayuwa ta gari.