Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya) a matsayin Kwamishinan sabuwar ma’aikatar harkokin gida da tsaron cikin gida.
Naɗin ya gudana ne yayin ƙaddamar da sababbin shugabanni ga hukumomin ilimi na jihar, ciki har da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil; Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin sabuwar ma’aikatar wajen tabbatar da tsaron al’ummar Kano, tare da yin kira ga Manjo Janar Idris da ya yi amfani da ƙwarewar sa ta Soja wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
An kafa wannan ma’aikata ne watanni biyar da suka gabata amma ba a naɗa kwamishina ba har sai wannan lokaci.
Ana sa ran ma’aikatar za ta yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa zaman lafiya a Jihar Kano.