Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da fara rarraba ruwa daga Rumbun Ruwan Goron Dutse zuwa al’ummomi daban-daban da ke cikin birnin Kano.
Bikin ƙaddamarwar wanda aka gudanar ranar Litinin ya tabbatar da cewa, rumbun ruwan ya dawo aiki bayan shafe sama da shekaru 30 ba a amfani da shi yadda ya kamata.
Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Yusuf ya bayyana farfaɗo da rumbun ruwan a matsayin wani muhimmin mataki wajen inganta samar da ruwa da kuma farfaɗo da muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar.
Ya ce dawo da rumbun ruwan cikin aiki na daga cikin manyan ƙoƙarin gwamnatinsa na magance matsalolin da suka daɗe suna addabar mazauna jihar, tare da inganta samun tsaftataccen ruwan sha.
A cewarsa, fara rarraba ruwa daga Goron Dutse zai taimaka wajen ƙara yawan ruwan sha da ake samu a sassan birnin Kano.
Shi ma Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dahiru Hashim, ya ce fara rarraba ruwan na daga cikin matakan da za su taimaka wajen inganta inganci da ɗorewar samar da ruwan sha na gwamnati a cikin birnin.














