Marafan Gonin Gora da ke a karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna, Alhaji Kabir Abubakar Danladi ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na da laifi kan hauhawan farashin kayan masarufi a kasar nan.
A hirarsa da LEADERSHIP Hausa a Kaduna, basaraken ya yi nuni da cewa laifin gwamnatin shi ne, rashin shiga a cikin al’amuran ‘yan kasuwar kasar nan don ta taka musu birki.
- Nijeriya Da Jamhoriyyar Benin Za Su Hada Kai Don Inganta Harkokin Kasuwanci
- Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa
Alhaji Kabir wanda kuma shi ne shugaban kungiyar da ke wanzar da zaman lafiya a tsakanin matasa, ya ci gaba da cewa kamar yadda ‘yan kasuwar ke fakewa da tashin farashin dala suna kara farashin kayan, kamar yadda kowa ya sani, dala tana hawa ne tana sauka, wasu ‘yan kasuwar, musamman kanana ba masu taba ganin dalar ba.
Ya kara da cewa, kamata ya yi idan farashin dalar ya sauka, suma ‘yan kasuwar sai su rage farashin kayansu, amma a kasar nan duk abun da farashinsa ya karu ba fa zai kara saukowa ba.
Kazalika, Kabir ya ce ‘yan kasuwar suna amfani da wannan damar ce don su tara abun duniya, inda ya ci gaba da cewa, kayan da ‘yan kasuwar ke sawo har yanzu suna nan a cikin shagunansu tsawon watanni.
Ya ce, abun bakin ciki idan sun tashi sai su sayar da su a matsayin sabon farashin, idan ka yi masu magana sai su ce maka ai sun sawo kayan ne a sabon farashi.
Ya ce a lokacin mulkin soji na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari an kayyade farashin kayan masarufi, haka ya kamata a wannan mulkin na dimokiradiyya ana da damar a yi hakan, domin ‘yan Nijeriys ne suka zabi gwamnatin.