Bayan tabbatar da barkewar annobar murar tsunitsaye a jihar Legas da Osun da Bayelsa, gwamnatin tarayya ta bukaci masu kiwo a kasar nan, musamman a wadannan jihohin hudu da su daukin matakan da suka kamata domin a dakile yaduwar annobar zuwa sauran guraren da ake yin kiwo a kasar nan.
Kungiyar likitocin dabbobi ce ta gano barkewar annobar a cikin watan Okutobar wannan shekarar.
- Asirin Namiji Mai Zamba Da Shigar Mata Ya Tonu
- Jam’iyyar APC A Kano Na So A Hukunta Bashir Ahmad Kan Halartar Gasar Cin Kofin Duniya A Qatar
Wannan bukatar ta gwamnatin na kunshe ne a cikin wata wasika da Dakta Maimuna Abdullahi Habib, Darakta a sashen kula da lafiyar dabbobi da kare yaduwar cutukan da ke harbin dabboni ta ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya ta aike wa da daukin daraktocin hukomomin kula da kiwon lafiyar dabbobi da ke a jihohin kasar nan 36 har da Abuja a makon da ya wuce akan maganar barkewar annobar.
Dakta Maimuna ta sanar da cewa, barkewar cutar a jihohi 29 a watan Janairun shekarar 2021 an dan samu tazara mai tsawon lokaci, inda ta ci gaba da cewa, gwajin da aka yi a kwanan baya, ya tabbatar da sabuwar barkewa cutar da kuma yaduwar ta, a saboda haka, ya zama wajibi a dauki matakan dakile ci gaba da yaduwar ta zuwa sauran guraren da ake kiwata Kajin na gidan gona a kasar nan.
A cewar Dakta Maimuna, bisa kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi na daukar matakan dakile yaduwar cutar ta samar da wani, tsari na sanya a duba guraren da ake kiwata Kajin na gidan gona, inda bincike ya nuna cewa, wasu masu kiwon Kajin na gidan gona ba sa bin matakan da ya dace na yin kiwon musamman yadda suke gwamatsa Kajin a wajen daya da kuma rashin yi musu allurar riga-kafi a lokacin da ya kamata.
“Ya zama wajibi a dauki matakan dakile ci gaba da yaduwar ta zuwa sauran guraren da ake kiwata Kajin na gidan gona a daukacin fadin kasar nan”.
Dakta Maimuna ta ci gaba da cewa, sauran matsalolin da aka gano sun hada da, rashin kula da Kajin da wasu masu kiwata su ba sa yi yadda ya dace wajen hada Kajin da sauran tsitsayen da suke kiwata wa duk a waje daya, jinkirin da ake samu wajen fitar da sakamakon gwajin Kajin na gidan gona da ake gani ba su da lafiya, jigilar kwan Kajin da masu hada-hadar kasuwancinsa ke yi a cikin mota daga arewacin Nijeriya zuwa kudancin kasar nan.
“Ina kira ga masu kiwon da sauran masu ruwa da tsaki a fannin da su guje wa yin kiwon ba bisa ka’ida ba domin a gujewa tada cutar zuwa ga sauran gidajen gona da ake kiwata Kajin na gidan gona a daukacin fadin Nijeriya”.
Daraktar ta yi kira ga masu kiwon da sauran masu ruwa da tsaki a fannin da su gujewa yin kiwon ba bisa ka’ida ba domin a gujewa tada cutar zuwa ga sauran gidajen gona da ake kiwata Kajin na gidan gona a daukacin fadin Nijeriya.