ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Ƙara Albashin Ma’aikatan Lafiya Da Kashi 95

by Sulaiman
1 month ago
Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin kashi 95 cikin 100 na albashin ma’aikatan lafiya a faɗin jihar, inda sabon tsarin biyan kuɗin ya fara aiki daga ranar 7 ga Satumba, 2026.

Gwamnatin jihar ta ce, sabon tsarin albashin ya yi daidai da tsarin albashin ma’aikatan lafiya da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, musamman Consolidated Health Salary Structure (CONHESS), wato Tsarin Haɗaɗɗen Albashin Ma’aikatan Lafiya.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Zamfara, Shehu Baraya, ne ya sanar da ƙarin albashin a cikin wata takardar umarni da aka fitar ranar 10 ga Satumba, 2026, mai lamba HS/Z/001/54/VOL.II.

ADVERTISEMENT

An aika takardar ga manyan jami’an gwamnatin jihar, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jiha, kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, sakatarorin dindindin da shugabannin ma’aikatu, sassa, hukumomi, hukumomin gudanarwa da kwamitoci.

Gwamnatin ta ce an sake duba tsarin albashin ne a wani mataki na inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

A cewarta, ƙarin albashin na da nufin ƙarfafa ma’aikatan lafiya, inganta jin daɗinsu da kuma samar da ingantattun yanayin aiki.

Ta ce ana sa ran ƙarin albashin zai ƙara wa ma’aikatan ƙwarin gwiwa da himma, tare da inganta ayyukansu da ingancin harkokin kiwon lafiya.

Sai dai gwamnatin ta buƙaci ma’aikatan lafiya su mayar da martani ga wannan ƙarin albashi ta hanyar ƙara jajircewa, ƙwarewa da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu.

Ta kuma umarci ma’aikatan da su riƙa kiyaye lokutan aiki na hukuma, bin ƙa’idar ladabtarwa da kuma yin aiki bisa dokoki, ƙa’idoji da ɗabi’un aikin gwamnati.

“Gwamnati na yaba da ci gaba da jajircewa da sadaukarwar ma’aikatan lafiya, kuma tana sa ran za su ƙara himma wajen gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya mai saurin amsa buƙatun jama’a a Jihar Zamfara,” in ji takardar.

Gwamnatin ta kuma umarci shugabannin ma’aikatu, sassa da hukumomi da su sanar da ma’aikatan da abin ya shafa sabon tsarin albashin, tare da tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan manufofin sake fasalin albashin.

Takardar ta ƙunshi sabon tsarin albashin CONHESS na asali da ya shafi matakai da digiri daban-daban, tare da alawus ɗin haɗarin aiki ga ma’aikatan lafiya masu aikin jinya kai tsaye da waɗanda ba sa gudanar da ayyukan jinya kai tsaye.

A sabon tsarin alawus ɗin haɗarin aiki, ma’aikatan lafiya masu aikin jinya da ke matakin albashi na 1 zuwa 5 za su karɓi N15,200, yayin da takwarorinsu da ba sa aikin jinya kai tsaye za su karɓi N14,250.

Ga ma’aikatan da ke matakan albashi na 6 zuwa 12, alawus ɗin zai kasance N30,400 ga masu aikin jinya, yayin da waɗanda ba sa aikin jinya kai tsaye za su karɓi N28,500.

Ma’aikatan da ke matakan albashi na 13 zuwa 15 kuma za su karɓi N32,300 a matsayin ma’aikatan lafiya masu aikin jinya, yayin da waɗanda ba sa aikin jinya kai tsaye za su karɓi N30,400.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair

MASU ALAKA

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani
Labarai

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

October 24, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Next Post
Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

Xi Ya Mayar Da Amsar Wasikar Daliban Jami’o’in Amurka

LABARAI MASU NASABA

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna

October 24, 2026
Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

Zaɓen 2027 Ba Kamar Na 2023 Ba Ne, Wannan Karon Ƙuri’un Kaduna Na Tinubu Ne — Gwamna Uba Sani

October 24, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 245, Ta Raba 214,997 Da Muhallansu A 2026 – NEMA

October 24, 2026
Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.