A kwanan nan, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya mayar da amsa ga dalibai daga jami’o’in Amurka guda 10, wadanda suka rubuta masa wasika bayan sun halarci shirin musayar matasa a kasar Sin.
Xi ya bayyana farin cikinsa da jin cewa daliban sun ji dadin ziyararsu a kasar Sin, wadda za su ci gaba da tunawa da ita.
Shugaba Xi ya ce, ya yi farin cikin da jin cewa a cikin wasikar, daliban sun yaba da wayewar kan kasar Sin, da fatansu na ganin an samu hadin gwiwa na abota mai karfi tsakanin kasar Sin da Amurka, da kuma muradinsu na zama jakadun sada zumunta tare da gina gadar da za ta hade Tekun Pacific.
Ya kuma bayyana fatan cewa, daliban za su bi sahun dimbin matasa na kasashen biyu wajen ci gaba da ingantawa da kuma karfafa hadin gwiwar abota mai zurfi tsakanin Sin da Amurka, tare da yin aiki tare don bunkasa fahimtar juna da kara kusanci a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, da kuma tabbatar da ci gaban alakar kasashen biyu ta dogon zango ba tare da tangarda ba, domin bayar da gudummawar kuzarin matasa wajen gina duniya mai dadin zama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














