Saboda nuna jagoranci mai cike da hangen nesa da kula da muradun al’umma tare da sauya Jihar Kebbi ta fuskar ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro, gyare-gyaren ma’aikatun gwamnati, ƙarfafa wa mata da kuma sabunta birane tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023. Nasir Idris Shi Ne Gwamnan Shekara Ta 2026A cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Kwamared Nasir Idris, Kauran Gwandu, ta aiwatar da wani gagarumin shirin raya jihar domin inganta jin daɗin jama’a da kuma sauya Jihar Kebbi a muhimman fannoni.
A fannonin ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro, jin daɗin ma’aikata, sabunta birane da ci gaban al’umma, gwamnatin ta aiwatar da matakai domin ƙarfafa wa hukumomin gwamnati, bunƙasa harkokin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar ’yan ƙasa.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi bayyana a cikin shirin raya jihar na gwamnatin shi ne zuba jari a ababen more rayuwa da sabunta birane. Manyan ayyukan gini da gyaran hanyoyi, tsarin magudanan ruwa, sanya fitilun kan tituna masu amfani da hasken rana, da kuma ƙawata wuraren jama’a sun sauya yanayin garin Birnin Kebbi da wasu garuruwa da dama.Kammala katafariyar Sakatariyar Bola Ahmed Tinubu da ke Gwadangaji, tare da farfaɗo da Hukumar Sufuri ta Jihar Kebbi da sabbin motocin bas 50, na nuna ƙoƙarin gwamnatin wajen inganta ayyukan gwamnati da sufuri. Gina katafaren Central Motor Park na zamani a Birnin Kebbi ya kuma ƙara inganta harkokin kasuwanci da sufuri.
A fannin kiwon lafiya, Gwamna Idris ya mai da hankali wajen inganta samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya masu sauƙin kuɗi. An farfaɗo da kuma inganta manyan asibitoci, cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ƙananan cibiyoyin lafiya, yayin da dubban ’yan ƙasa masu ƙaramin ƙarfi suka amfana da shigar da su cikin tsarin inshorar lafiya na jihar da sauran shirye-shiryen tallafi da ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar abokan ci gaba.
Domin magance ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, gwamnatin ta ɗauki ma’aikatan lafiya sama da 2,000, ciki har da likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya. Haka kuma, an zuba jari wajen samar da kayan aikin lafiya, inganta cibiyoyin kiwon lafiya da samar da motocin ɗaukar marasa lafiya, domin ƙarfafawa ayyukan kiwon lafiya da dawo da amincewar jama’a ga cibiyoyin kiwon lafiya mallakar gwamnati.
Jin daɗin ma’aikata da gyare-gyaren ma’aikatan gwamnati sun kasance cikin muhimman abubuwan da gwamnatin ke bai wa fifiko. Gwamnati ta ci gaba da biyan albashi a kan lokaci tare da magance basussukan fansho, garatuti, kuɗaɗen tallafin rasuwa da sauran haƙƙoƙin ma’aikata da aka gada daga gwamnatocin baya. Aiwatar da mafi ƙarancin albashin Naira 75,000, tare da shirye-shiryen ƙara ƙwarewar ma’aikata da sauran matakan jin daɗi, ya nuna yadda gwamnatin ta fahimci muhimmancin samun ma’aikatan da ke da ƙwarin gwiwa da kuma iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ɗaukar malamai sama da 2,000, samar da gidaje masu rahusa ga ma’aikata da kuma kawo ƙarshen tsarin ɗaukar ma’aikata na wucin gadi a ma’aikatan gwamnati, na daga cikin matakan inganta mutuncin ma’aikata, tsaron aikin yi da ƙara yawan aiki.
A matsayinsa na tsohon malamin makaranta, Gwamna Idris ya kuma mai da hankali sosai kan ilimi. Matakan da suka haɗa da ƙara shekarun ritayar malamai da tsawon shekarun da za su yi aiki, ɗaukar ƙwararrun malamai bisa cancanta, gyaran makarantu da samar da kayan ɗaki, sun taimaka wajen inganta yanayin koyo. Gwamnatin ta kuma ci gaba da biyan manyan kuɗaɗen jarabawa, ciki har da WAEC, NECO, NABTEB da NBAIS, tare da ƙara kuɗaɗen ciyar da ɗaliban makarantun kwana.
Haka kuma, ana gina manyan makarantu masu haɗa ilimin yau da kullum da na sana’o’i a manyan masarautu, a wani ɓangare na babban shirin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi da bai wa matasa ƙwarewar da ta dace da rayuwa da kasuwanci.
Noma, wanda shi ne babban ginshiƙin tattalin arzikin Jihar Kebbi, ya samu kulawa sosai ta hanyar shirye-shiryen tallafa wa manoma da ƙarfafa samar da abinci. A ƙarƙashin Kauran Gwandu Agricultural Deɓelopment Agenda, an raba takin zamani, ingantattun iri da magungunan noma ga manoma. Gwamnatin ta kuma inganta aikin noma ta amfani da injuna da tsarin ban ruwa, ta hanyar shirye-shirye kamar sauya injinan famfunan ruwa masu amfani da man fetur zuwa waɗanda ke amfani da LPG, tare da raba famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana. Gina hanyoyin karkara ya taimaka wajen haɗa al’ummomin manoma da kasuwanni tare da rage asarar amfanin gona bayan girbi.
A lokaci guda, shirin Residual Moisture Crop Production ya mayar da wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa zuwa yankunan da ake samun amfanin gona mai yawa.
Tsaro ya kasance babban abin da gwamnatin ke bai wa fifiko, musamman a al’ummomin da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka suka addaba. Gwamnatin ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta na cikin gida, ta hanyar samar musu da motocin aiki, babura, kayan aiki da sauran tallafi.
An tura motocin sintiri Hiluɗ sama da 100 domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa na tabbatar da tsaro, yayin da dubban jami’an sa-kai suka samu horo, ƙarfafawa da kayan aikin gudanar da ayyukansu. Waɗannan matakai sun inganta sa ido da tsaro a wuraren da matsalar ta fi ƙamari, lamarin da ya bai wa manoma da dama damar fara komawa gonakinsu a hankali, tare da bai wa al’ummomi damar samun ƙarin kwanciyar hankali.
Gwamnatin ta kuma aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi mata, matasa, yara da sauran masu rauni, ta hanyar koyar da sana’o’i, horas da dabarun dogaro da kai, tallafa wa harkokin kasuwanci da sauran shirye-shiryen jin daɗin jama’a. Tallafa wa marayu da yara masu rauni, gyaran cibiyoyin jin daɗin jama’a da kuma ci gaba da gudanar da shirin auren jama’a na shekara-shekara, na nuna yadda gwamnatin ke ba da muhimmanci ga haɗa kowa cikin ci gaba da kuma tallafa wa ’yan ƙasa marasa galihu.
A cikin shekaru uku, gwamnatin Nasir Idris ta kafa tarihi a fannoni daban-daban na shugabanci. Duk da cewa akwai sauran ƙalubale da buƙatun raya ƙasa, matakan da aka aiwatar a fannonin ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro, jin daɗin ma’aikata da ci gaban al’umma, sun nuna ci gaba da jajircewar gwamnati wajen gudanar da shugabanci me mai da hankali kan jama’a da kuma sauya Jihar Kebbi.Sauran ayyukan gwamnatin da suka shafi bunƙasa matasa, wasanni, kasuwanci, albarkatun ruwa, raya karkara, al’adu da sauran fannoni, sun ƙara nuna faɗin ajandar ci gaban da gwamnatin ta sanya a gaba.
Haƙiƙa, a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, Jihar Kebbi ta ci gaba da tafiya a kan turbar sabuntawa, wadda aka gina bisa bunƙasa ababen more rayuwa, gyare-gyaren hukumomi da shirye-shiryen inganta jin daɗi da wadata ga al’ummar jihar.














