Al’ummar Ƙaramar Hukumar Tambuwal da ke Jihar Sakkwato sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Juma’a, inda suka yi kira ga Gwamnatocin Tarayya da Jiha da su gaggauta ɗaukar mataki kan matsalar tsaro.
Masu zanga-zangar sun ce hare-haren ’yan bindiga sun tilasta wa ɗaruruwan mazauna ƙauyuka barin gidajensu zuwa Tambuwal domin neman mafaka.
Sun ce kisan mutane, garkuwa da mutane, satar shanu da dukiyoyi, da kuma tilasta wa jama’a biyan haraji ga ’yan bindiga na ci gaba da addabar yankin.
Hakan ya kawo cikas ga noma, kasuwanci da zirga-zirga.
Matsalar ta kuma shafi Ƙananan Hukumomin Kebbe da Shagari da ke maƙwabtaka da Tambuwal, inda hare-haren ’yan bindiga suka sa wasu jama’a barin garuruwansu.
A ranar Alhamis, ’yan bindiga sun sace wani ma’aikacin INEC da ke aiki a Tambuwal a garinsu na Girkau, Ƙaramar Hukumar Kebbe, inda suka kashe mutum ɗaya.
Rundunar ’Yansandan Sakkwato ta tabbatar da cewa tana sane da lamarin.
Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya ce jami’an tsaro na ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.














