Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aikin ƙasa baki ɗaya idan Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka gaza magance matsalolin da suka shafi aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar, da kuma biyan basussukan albashi da alawus-alawus.
ASUU ta ce wasu jami’o’in gwamnati, musamman na jihohi, har yanzu ba su aiwatar da muhimman tanade-tanaden Yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2025 ba, duk da cewa yarjejeniyar ta fara aiki tun daga Janairun 2026.
Ƙungiyar ta kuma yi korafin rashin biyan wasu alawus-alawus, da basussukan karin albashi da na karin matsayin ma’aikata, da kuma wasu kuɗaɗen da ake cirewa daga albashin malamai amma ba a miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa ba. A wasu jami’o’i kuwa, malamai sun riga sun fara yajin aiki saboda rashin biyan albashi da sauran hakkokinsu.
A Jami’ar Sule Lamido da ke Jihar Jigawa, reshen ASUU ya bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu ta biya basussukan da ake bin malamai tare da aiwatar da yarjejeniyar, ko kuma a fara yajin aiki daga 15 ga Satumba 2026.
ASUU ta ce idan gwamnatoci ba su dauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya sake haifar da tsaiko a harkokin karatu a jami’o’in ƙasar. Ƙungiyar ta kuma bukaci gwamnatoci su cika alkawurran da suka dauka domin kauce wa sabon rikicin da zai shafi ɗalibai da tsarin ilimin jami’a.














