Ƙungiyar Kiristocin Arewa (NCA) ta yi Allah-wadai da sabbin hare-haren da aka kai a Jihar Filato, inda ta gargaɗi ’yan Nijeriya da ka da su saba da tashin hankali har mutuwar mutane ta zama ba a bakin komai ba.
Ƙungiyar ta ce aƙalla mutane tara ne aka kashe a hare-haren da aka kai wasu sassan Barkin Ladi, Riyom da wasu garuruwa tsakanin daren Asabar da safiyar Lahadi.
A cewar ƙungiyar, matafiya biyar da ke kan hantarsu ta zuwa Gana-Ropp a Barkin Ladi sun mutu bayan da aka kai wa motarsu hari.
Haka kuma, an kashe wani fasto da wani mutum yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa coci a Dorowa Babuje.
An kuma samu rahoton wasu hare-hare a Baten Wereng da Ratyidi.
Shugaban NCA, Rev. Joseph John Hayab, ya ce duk ran wanda aka rasa babban rashi ne da ya kamata gwamnati da ’yan Nijeriya su damu, ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko siyasa ba.
Ya yi kira da a inganta tattara bayanan sirri, samar da tsarin gargaɗi tun da wuri da kuma ƙara haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin yankunan domin daƙile hare-haren.
Hayab ya kuma buƙaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike kan hare-haren, su kama waɗanda ke da hannu sannan a gurfanar da su a gaban kotu.
Ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe tare da kira ga gwamnati da ta tallafa wa mutanen da hare-haren suka shafa.














