Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba kujerun zama masu mazauni uku-uku guda 73,800 ga makarantun jihar da ke kananan hukumomi 44.Â
Wannan wani bangare ne na kudurinsa na inganta ilimi biyo bayan kaddamar da Dokar Ta-Baci kan Ilimi, domin tabbatar da cewa kowane yaro a Kano ya samu ingantaccen ilimi.
- ‘Yan Nijeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Tsadar Iskar Gas
- Dubun Wani Dan Shekara 74 Da Ake Zargi Da Sace Tabarmi A Masallaci Ta Cika
A wajen cibikin rabon da aka gudanar a Cibiyar Kasuwanci ta Kano, Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin samar da kayan makaranta domin taimaka wa dalibai wajen mayar da hankali domin samun nasara.
Ya bayyana cewa kujerun wadanda aka kera su da inganci, za su amfani daliban da ke makarantu a jihar da ma wasu da za su zo a nan gaba.
Gwamnan, ya kuma gode wa matasa sama da 11,000, masu sana’ar kafinta da walda, wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kammala aikin a kan lokaci.
Har wa yau, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafa wa fikirar matasa da kuma karfafa musu.
A cikin wasu hotuna da Hadimin Kwankwasiyya Kan Kafofin Sadarwa, Ibrahim Adam, ya wallafa, an ga yadda gwamnan ke duba sabbin kujerun da aka kera.
Wannan na daga cikin alkawuran da Gwamna Yusuf ya dauka a yakin neman zaben 2023.
A lokacin ya ce zai inganta harkar ilimi a Kano ta hanyar samar da kayan aiki masu nagarta domin ci gaban jihar.
Ga hotunan yadda rabon ya gudana: