Wata takardar bayani da kasar Sin ta fitar yau Asabar, ta ce a shekarun baya-bayan nan, tsarin ilimin sana’o’i na kasar, yana samar da matsakaicin adadi na kwararrun ma’aikata miliyan 10 ga masana’antu daban-daban.
An fitar da takardar bayani kan ilimin sana’o’i na kasar Sin ne a taron kasa da kasa na 2026 kan raya ilimin fasahohi da sana’o’in hannu, wanda ya gudana daga ranar Alhamis zuwa yau Asabar, a birnin Tianjin na kasar Sin.
Takardar ta kuma bayyana cewa, matsakaicin tsawon lokacin karatu na sabbin kwararrun ma’aikatan na Sin, ya kai shekaru 14.35. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














