Fu Cong, zaunannen wakilin Sin da ke MDD, ya jaddada bukatar bin tsarin da kasashen Afirka ke jagoranta domin cimma mafita ta siyasa ga rikicin kasar Sudan.
Fu Cong ya bayyana hakan ne jiya Jumma’a, yayin wani taron Kwamitin Sulhu na MDD kan nazarin halin da Sudan ke ciki.
Fu ya ce, kasar Sin ta dade da rike matsayi mai adalci game da batun Sudan, kuma ta yi kira da a kawo karshen rikicin da wuri. Ya ce tun bayan barkewar rikicin, kasar Sin ta samar da tallafin kayayyaki iri-iri ga Sudan, wadanda suka hada da abinci, kayayayyakin likitanci, da kayayyakin ceton jama’a da sauransu. Kuma za ta ci gaba da bayar da taimako gwargwadon karfinta, tare da taka rawar gani wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan.
A wannan rana kuma, a gun wani taro mai taken “Duniya a nan gaba: Sake gina aminci ta hanyar daukar matakai kan sauyin yanayi”, wanda shugaban babban taron MDD ya shirya, Fu Cong ya yi kira da a karfafa tsarin shugabancin yanayin duniya, tare da hanzarta aiwatar da sauyi zuwa tsarin muhalli mai tsafta. Ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka rawar gani wajen ingantawa da bayar da gudummawa ga ayyukan kula da yanayin duniya, inda ta shiga hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye muhalli tare da kasashe da yankuna sama da 100, wanda hakan ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi. (Safiyah Ma)














