Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi yawan yawace-yawace da wasu matan ke yi, duba da yadda wasu matan ke da dabi’ar yawace-yawace a kullum zuwa gidajen makofta, musamman wadanda suke da aure, domin su yi hira.
- Babu Wani Annabi Mai Daraja Kusa Da Ta Muhammad Rasulullah (SAW)
- Danyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.436 —OPEC
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce akan hakan?, me yake janyo haka, kuma me ya sa?, ko akwai wasu illoli ko amfanin yawan yawace-yawace?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), daga Jihar Kano:
Kwarai akwai, musamman sababbin unguwanni, nan sai ki samu sama da mace goma sun taru gidan mace daya. San gantali ne da zaman gulma kawai. Ba shi da amfani karshe ma dai a koyo wasu dabi’u na daban. Su daina tun kan su girgide aurensu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
Tabbas hakan ana samun wasu matan da irin wannan dabi’a, kuma hakan na haifar da matsaloli da dama a zamantakewa. To, magana ta gaskiya sakacin mai gida a lokuta da dama shi ke jawo wannan matsala, to amma a wasu lokutan matan suna yin hakan bada sanin maigidan ba wato suna yin satar fita. Hakika illolin suna da yawa, na farko za ta zama munafuka wasu lokutan kuma a dora mata sata da dai sauran su. amfani kuwa babu wani amfani a wannan dabi’a face zubar da mutunci. To, shawara ta a nan ita ce su ji tsoron Allah matan su daina wannan dabi’a, maza kuma ya kamata mutum yake kula da abubuwan dake faruwa a gidan sa sosai.
Sunana Princess Fatima Mazadu, Gomben Nijeriya:
Yin hakan ba abu ne me kyau ba, ya kamata mace ta kare hakkin aurenta ba yawace-yawace ba. Hira ba dole bane sai an fita yi, tun da akwai karance-karance na alkur’ani ko littatafai ko sauraron rediyo, ba amfanin tsallake muhalli zuwa na wani daban. Ko da mutun bai ce kina takura shi ba, ko dan gulma da hirar karya, da koyan sababbin dabi’au marasa kyau, da munafunci, ke kanki bai dace ba a tsarance. Ya kan janyo rashin kamun Kai, zubda mutunci da da-na-sani, saboda a cikin magana zat a fadi sirrinta a zo ana yayatawa tana takaici. Wata ma aurenta har mutuwa yake yi, saboda ba kowa zai dauki mace mai yawan yawo da mutunci ba. Shawarata a nan mata a rika hakuri a gidan aure, in damuwace ki roki Allah, kowa da irin tasa jarabawar, ki rungumi taki hannu bibbiyu, saboda ki tsira da mutuncinki. Allah ya yasa mu dace.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
Hakan bai kamata ba, saboda duk hirar da mace za ta yi a cikin gida tare da mutane karshe a kawo hirar wata, ko a hada wani munafurcin, musamman idan mace tana da kishiya ko facala. Ba za ta zauna a gidanta ba, sai dai ta rika yawo tana fadar halayyar ta ko tana bata ta. Hakan yana kawo matsaloli da yawa, wani zai iya raba aurenta dalilin yawo aure yakan iya mutuwa. Shawarata macen aure ta zauna a gidanta ta fahimci aurenta, ta fuskanci aurenta, da yi wa mijinta biyayya, in sana’a take ta mayar da hankakinta a kai ya fi yawo da yawan shiga makota da gidajen mutane.
Sunana Muktari Sabo, Jahun Jihar Jigawa:
Tabbas akwai mata masu irin wannan dabi’a ta yawace-yawace wanda hakan ba daidai bane, ko da shiga gidan makwafta ne. Rashin girmama aure da kuma rashin sanin darajar kai shi ke janyo hakan, Illar wannan shi ne zai sa mace ta zamo mai hada husuma da kuma rashin godiya a gidanta. Sannan ga zubewar darajarta da ta ‘ya’yanta a idon mutane. Shawara a nan shi ne mata masu wannan hali su ji tsoron Allah, su sani hakan yana jawo fushin Allah subhanahu wa ta’ala.
Sunana Anas Bn Malik, Achilafiya, Karamar Hukumar Ƴankwashi, Jihar Jigawa:
Yawace-yawacen mata zuwa gidajen makwabta na iya zama al’ada mai kyau idan ana yin sa cikin mutunci da iyaka, domin yana karfafa zumunci, taimako da musayar ilimi. Amma idan ya wuce kima, yana iya jawo matsaloli kamar bata lokaci, sakaci da gida, shiga cikin gulma ko rikici, da kuma karya sirri. Sau da yawa dalilan da ke janyo hakan sun hada da; rashin aikin yi, neman nishadi, ko bukatar goyon bayan al’umma. Don haka shawarar da ta fi dacewa ita ce a daidaita wannan dabi’a: a tsara lokaci, a mutunta iyaka da sirrin makwafta, a guji gulma, sannan a mayar da hankali kan nauyin gida da tarbiyya. Wannan zai sa zumunci ya dore ba tare da matsala ba.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Wasu gaskiya ya fara tun daga gida kafin su yi aure, kodayaushe in ka je basa gida sai gidan makota basa iya zama a gida ko kadan. Gaskiya sabo ne tun kafi aure iyaye basa magana shi ne har gidan miji, mace bata iya zama dakinta. Gaskiya hakan ba shi da wani amfani ko kadan. Shawarata ga masu irin wanan hali dan Allah su daina, ba shi da wani anfani yin hakan. Kuma iyaye su yi kokarin hana wanan yawon tun kafin su ba da auren ‘yar su, saboda yara amana ce Allah ya basu, Allah ya bamu ikon gyarawa (Amin).
Sunana Muhammad Isah Zareku, Miga A Jihar Jigawa:
A gaskiya wannan tana faruwa za ka ga mata sun ki zaman gidan aurensu suna shiga gidajen makwafta ba dan komai ba sai don hira da kuma zancen mutane kawai. Hakan yana kawo matsala ka ga mace taki zaman gidanta kawai don son zancen mutane. Kuma hakan yana kai su gidan makwafta ne don munafurci. Illolinsa ya fi yawa saboda a wannan shige da fice na shiga makwafta yake kawo rashin jituwa a makwabta, kuma ni a nawa tunanin ba shi da wani amfani yawan shiga gidan makwafta. Shawara a nan ita ce, mace ta zauna a gidanta duk wacce za ta je wajenta ita zaman auren take, don me ya sa za ki bar naki gidan ki tafi nata haka kawai.













