Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi ƙarin bayani kan cire sunayen wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnonin jihohi na 2027.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a shari’ar da ta haɗa INEC da Jam’iyyar Zenith Labour Party, mai lambar ƙara SC/CV/495/2026, a ranar 24 ga Satumba, 2026.
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da INEC ta ɗaukaka zuwa Kotun Ƙoli kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadda ta soke tanade-tanaden Sashe na 77 (5–7) na Dokar Zaɓe ta 2026. Waɗannan tanade-tanade sun wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu a matsayin sharadin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani.
Sai dai Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa tanade-tanaden Sashe na 77 (5–7) na Dokar Zaɓe ta 2026 sun yi daidai da Kundin Tsarin Mulki, kuma wajibi ne dukkan jam’iyyun siyasa su bi su.
Kotun ta kuma tabbatar da sahihancin Mataki na 2 na jadawalin ayyukan zaɓe na INEC, wanda ya wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu tsakanin ranar 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.
Bugu da ƙari, Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar siyasa da ta gaza bin tanade-tanaden Sashe na 77 (5–7) ba za ta cancanci tsayar da ɗan takara a zaɓen ba.
INEC ta bayyana cewa ta yi amfani da wannan hukunci wajen kammala jerin sunayen ’yan takarar gwamna, bisa tanadin Sashe na 287 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.
Hukumar ta ce ta cire jam’iyyun siyasa da suka gaza bin tanade-tanaden dokar dangane da tsayar da ’yan takara.
Sai dai INEC ta bayyana cewa ta riga ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 12 ga Satumba, 2026, kwanaki 13 kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin.
A cewar hukumar, Sashe na 32 (2) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya bai wa jam’iyyun siyasa da suka yi imanin cewa an cire sunayen ’yan takararsu ba bisa ƙa’ida ba damar sanar da INEC cikin kwanaki 14 daga ranar wallafa jerin sunayen.
INEC ta ce wa’adin ƙarshe na gabatar da irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe shi ne ranar 24 ga Oktoba, 2026.
Hukumar ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya, bin doka da oda, da kuma sahihancin tsarin zaɓe a Nijeriya.














