A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da shugaban Botswana Duma Gideon Boko a Beijing, sannan suka halarci bikin sanya hannu kan daftarorin hadin gwiwa tsakanin kasashensu.
Shugaba Duma Gideon Boko na ziyara a kasar Sin daga ranar 12 zuwa 17 ga wata. Wannan ita ce ziyararsa ta farko a kasar Sin tun bayan kama aiki a matsayin shugaban kasar Botswana.
A nasa bangare, ministan kula da harkokin wajen Botswana Phenyo Butale, ya bayyana yayin hirar da ya yi da kafar CMG a birnin Gaborone a baya-bayan nan cewa, Botsawana na daukar dangantakarta da Sin da matukar muhimmanci, kuma tana sa ran kara zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan bangarori.
Har ila yau a yau Talata, shugaban kasar Sin ya gana da shugaban majalisar ministocin kasar Togo, Faure Essozimna Gnassingbe, a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














