A yau Laraba ne jiragen fasa dusar kankara na kasar Sin wato Xuelong da Xuelong 2, ko kuma Snow Dragon da Snow Dragon 2 suka komo birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, bayan shafe kusan watanni uku a balaguron binciken yanayi karo na 16 a yankin tekun Arctic.
Jiragen sun yi nasarar kammala muhimman ayyuka, wadanda suka hada da cikakken bincike da sanya idanu, hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kuma karfafa binciken kimiyya, inda tawagar masu binciken ta shaida cewa an samu nasara sosai a duka binciken da aka gadunar.
An cimma gagarumar nasara yayin balaguran, musamman ta fuskar gano sabbin abubuwa na kimiyya, da gagarumin ci gaba a fahimtar ka’idojin nazarin kimiyya, da gwaje-gwajen fasaha da amfani da kayan aikin bincike wadanda za su taimaka wajen fahimta da kuma magance kalubalan sauyin yanayi da kuma samar da ci gaba mai dorewa a yankin Actic.(Mai fassara: Suleiman Suleiman)














