ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Sin

A ranar Juma’ar da ta gabata, aka kaddamar da Kimi K3, wani samfurin kirkirrarriyar basira ta AI da kamfanin Moonshot AI na kasar Sin ya samar, wanda ya zama wata sabuwar nasara a fannin raya AI mai budadden tsari. Wannan nasara ta zo a daidai lokacin da Sin ta fara karbar bakuncin babban taron duniya kan AI da tsarin shugabancin duniya a bangaren amfani da AI.

Yayin taron, ra’ayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar kan dabarar kirkirarriyar basira ta AI shi ne, samar da fasahar AI mai mayar da hankali kan bukatun jama’a, wadda za a amince da ita, dake karkashin sarrafawar dan adam, kuma fasaha mai amfani da amfanar da kowa.

Ra’ayin ya samu karbuwa a wajen mahalarta da ma sauran al’ummar duniya, kuma ya nuna yadda Sin ke son fasahar mai saurin bunkasa ta zama wadda kowa zai amince da ita, ya kuma amfana, musammam kasashe masu tasowa da ke zama koma baya a duk lokacin da duniya ta samu wani sabon abu.

ADVERTISEMENT

A ganina, gibin da ake samu tsakanin kasashe manya da masu tasowa da ma yadda kasashe masu tasowa ke kasancewa a baya a duk lokacin da aka samu sabon abu, ya kusa zama tarihi, saboda kasar Sin tana gaba gaba a bangaren raya fasahar AI, kuma ita mai son tafiya ne tare da kasashen duniya ta yadda za a samu ci gaba da makoma ta bai daya ba tare da ware wani bangare ba.

Samfurin AI na Kimi K3 da kamfanin Sin ya samar, samfuri ne mai budadden tsari mafi girma a duniya. Haka kuma, ya shiga cikin tsare-tsaren AI dake kan gaba a duniya. Wannan na nufin sabanin irin wadanda tsare-tsarensu a rufe yake, ya samar da fasahar cikin rahusa ko kyauta ta yadda za a iya sauya tsarinta bisa bukatun da ake da su.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Karfin kasar Sin a bangaren fasahar AI ba zai iya misaltuwa ba, kuma irin wannan budadden tsari da za a iya aiwatar da sauye-sauye a cikinsa domin su dace da bukatun da ake da su, ya dace da ra’ayin da shugaban ya gabatar yayin bude taron duniya kan AI.

Ta wannan tsari, za a iya sanya harsuna da yanayi da tsare-tsare da bukatu daban daban, ta yadda za su dace da mabambantan kasashe ko yankuna ko al’ummomi. Kuma zai iya bayar da hidimomi a bangarorin bayar da ilimi, gargadin yanayi da ayyukan gona da kiwon lafiya da duk wani abu da aka ba shi horo kai domin biyan bukatun al’umma.

Da irin wannan AI mai budadden tsari na kasar Sin, kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afrika, ba zama masu amfani da fasahar kadai za su yi ba, za su samu damarmakin tsara fasahar, ta yadda za ta hidimtawa al’ummominsu, kuma kowa zai iya cin gajiyarta a duk inda yake cikin sauki.

Watau dai, su ma ba za a bar su a baya ba, za su shiga cikin jerin kasashen duniya masu cin gajiyar fasahar ta zamani. (Fa’iza Mustapha)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.