ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

by Abubakar Sulaiman
3 months ago
NAFDAC

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta tsananta ayyukan tabbatar da doka a Jihar Legas, inda ta bankaɗo jabun kayan shaye-shaye masu saurin bugarwa, da gurbatattun kayan abinci, da kuma yin amfani da manyan motocin dakon mai (tankers) ta hanyar da ke barazana ga lafiyar jama’a.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai game da wadannan sumame, Daraktan Bincike da Tabbatar da Doka na hukumar, Dr. Martins Iluyomade, ya bayyana cewa wannan kame na nuni da kudurin NAFDAC na kare lafiyar ‘yan kasa ta hanyar tabbatar da cewa kayayyaki masu kyau da amintattu ne kawai ke shiga kasuwa.

Badaƙalar Motocin Man Girki Da Aka Loda Wa Dizal

Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da hukumar ta samu shi ne tsare wasu manyan motoci guda biyu waɗanda aka keɓe na musamman domin jigilar man girki na alayyahu (edible vegetable oil), amma aka kama su maƙare da man dizal (Automotive Gas Oil).

ADVERTISEMENT

Dr. Iluyomade ya jaddada cewa wannan babban laifi ne da ke da haɗari mai yawa ga lafiyar abinci da bil’adama.

Yayin tambayoyi, manajan motocin ya yi da’awar rashin sanin dokar alamomin launi (colour-coding) da aka tanada don motocin man girki, sannan ya amsa cewa a baya ma ana amfani da motocin ne wajen jigilar dizal kawai.

LABARAI MASU NASABA

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

An tsare motocin da ma’aikatansu yayin da ake ci gaba da bincike.

Ƙera Jabun Giya

Hukumar ta kuma ruguza wasu masana’antun ɓoye guda biyu da ke ƙera jabun kayan shaye-shaye masu saurin bugarwa a yankin Mushin na Jihar Legas. Wannan sumame ya kai ga kama mutane biyu da ake zargi: Mr. Uchenna Ekezie da Mr. Peter Okparalgbo.

An kwato ɗimbin jabun kwalaben giya na shahararrun kamfanoni na gida da na ƙasashen waje daga shaguna da wuraren ajiyar da suke amfani da su.

Dr. Iluyomade ya shaida da cewa NAFDAC za ta ci gaba da sanya ido da gudanar da sumame a faɗin ƙasar nan, kuma yana kira ga jama’a da su rika siyan kayayyaki a wurare amintattu tare da kai rahoton duk wani motsi na zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.

NAFDAC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

MASU ALAKA

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya
Tsaro

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

October 28, 2026
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120
Labaran Kasuwanci

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

October 28, 2026
EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku
Siyasa

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

October 28, 2026
Next Post
Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

October 28, 2026
EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Zarge-Zargen Cin Hanci Kan Atiku

Shirin Tinubu Na Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 20.5 Ya Tabbatar Da Hasashena – Atiku

October 28, 2026
2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

2027: Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen NDC Ya Buƙaci Atiku Ya Marawa Tafiyar Obi-Kwankwaso Baya

October 28, 2026
Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Ayarin Motocin Gwamnan Neja A Minna

October 28, 2026
Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2026
An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

October 27, 2026
ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.