Mataimakin shugaban kasar Sin, Han Zheng, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Ghana domin aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma ci gaba da raya dadadden zumunci, da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwa a aikace, tare da ci gaba da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Ghana.
Han ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, a birnin New York, a gefen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81.
A nasa bangare, Mahama ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Ghana da Sin tana da tushe mai kwari na tarihi, kuma Ghana tana matukar godiya da kyakkyawan goyon baya da taimakon da Sin take bayarwa cikin shekaru da dama.
Mahama ya bayyana cewa, a kodayaushe Ghana tana bin manufar “kasar Sin daya tak a duniya” sau-da-kafa, kuma tana fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni irin su cinikayya, da zuba jari, da hakar ma’adanai da ayyukan masana’antu, tare da inganta musaya a tsakanin al’ummomin kasashen biyu domin ci gaba da habaka dangantakar da ke tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














