Rundunar ’yansandan Abuja ta kama wata matar aure, Rukayat Muhammed, bisa zargin ta da hannu a mutuwar wani mutum a wani otal da ke Gwarimpa.
Kwamishinan ’yansandan Babban Birnin Tarayya, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan ranar Asabar yayin wani taron manema labarai.
Ya ce iyalan marigayin ne suka fara kai rahoton ɓacewarsa, kafin daga bisani aka gano gawarsa a gefen titin Kubwa kusa da ƙarƙashin gadar Katampe, a ranar 26 ga watan Agusta 2026.
Binciken ’yansanda ya gano cewa marigayin ya yi magana da Rukayat kafin mutuwarsa.
Haka kuma, bincike ya nuna cewa ana zargin suna da alaƙa ta soyayya kuma sun zauna a otal ɗin Good Samaritan Guest House da ke Gwarimpa.
A cewar ’yansandan, Rukayat ta ce ta gano cewa mutumin ba ya numfashi.
Sai dai maimakon ta kai rahoton lamarin ga ’yansanda, an ce ta ɗauki wayarsa ta bar masaukin.
’Yansandan sun ce daga baya wasu ma’aikatan masaukin biyu sun gano gawarsa a ɗakin.
Ana zargin sun fitar da gawar zuwa Kubwa, inda suka jefar da ita.
An kuma kama ma’aikatan biyu, Ibrahim Omeiza da Kefat Bitrus, domin gudanar da bincike.
Kwamishinan ya ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya sanadin mutuwar mutumin ba.
Ya ce duk wanda bincike ya gano yana da hannu a mutuwar mutumin ko kuma wajen ɓoye da jefar da gawarsa, zai fuskanci hukunci bisa doka.














